Hajiya Salamatu Garba ita ce Shugabar kungiyar Ci gaban Mata Manoma ta kasa (WOFAN), a hirarsu da Aminiya ta ce rayuwar mata ba ta tsaya kawai ga abin da ya shafi haihuwa da raino ba, akwai batun inganta rayuwarsu ta hanyar samun ilimi da kula da lafiyarsu da kuma ‘ya’yansu.
Tarihin rayuwata
An haife ni a Jihar Kaduna. Na yi karatun firamare da sakandire a can. Na yi digiri na farko da na biyu a jami’ar Ahmadu Bello Zariya. Bayan na kammala hidimar kasa sai na fara koyarwa a makarantar sakandire ta kueen Amina. A shekarar 1984 kuma sai na koyar a tsangayar Kimiyyar Tsirrai (Plant Pathology) ta Jami’ar Ahmadu Bello Zariya har tsawon shekara takwas. Kasancewar maigidana dan Jihar Kano ne sai na nemi canjin aiki zuwa Jami’ar Bayero ta Kano, na ci gaba da koyarwa tsawon shekara bakwai, daga bisani na koma harkar kungiya gaba daya. Na samu kwarin gwiwa da masaniya a kan abin da ya shafi kafa kungiyoyi ne daga lokacin da na yi wani kwas kan raya jinsi (gender debelopment) a Jami’ar WaB Hunting da ke Birtaniya.
Iyali
Tun ina jami’a aji biyu na yi aure. A yanzu haka ‘ya’yana duk sun kammala karatu sun yi aure. daya likita, daya kuma malama ce a Jami’ar Bayero, yayin da dayar kuma ta karanta harkar noma. A yanzu haka ma ina da jikoki. Alhamdulillahi duk nasarar da na samu a rayuwa ta dogara ne da irin taimakon da maigidana ya ba ni, duk wani abu da zan yi a gida ko a wajen kasar nan yana ba ni goyon baya dari bisa dari. Idan ba haka ba babu inda zan je a rayuwa.
Abincin da na fi so
A da dai na fi son cin tuwon shinkafa da miyar taushe, sai dai yanzu da girma ya zo nakan ci kayan marmari da ganyayyaki a matsayin abinci. A yanzu kayan abincinmu irinsu shinkafa su dawa ba sa yin kamshi irin na da saboda yawan zuba taki da manoma ke yi. Ina tuna lokacin da idan ana tuwo a gida sai kowa ya sani saboda kamshi.
Mutanen da na koyi wani abu daga gare su
A gaskiya ire-iren wadanann mutanen suna da yawa. Ba zan iya cewa ga mutum daya ba, kasancewar a kowane bangare na rayuwa ina da irin wadannan mutane. Tun ina karama nake koyon wani abu daga kawayena wadanda suka girme ni. Shi ya sa za ka ga cewar yadda nake gudanar da rayuwata yana gaba da na sa’annina.
Tarihin kafuwar WOFAN
Tun ina koyarwa a ABU na yi tunanin kafa kungiyar WOFAN, a lokacin mun je wani aiki ne a wani kauye cikin karamar Hukumar Ikara da ke Jihar Kaduna, sai na ga wata mata mai tsohon ciki tana dawowa daga gona ga kaya niki-niki a kanta, ga kuma dabbobi suna biye da ita. Wannan ya sa tausayi ya kama ni, har na raka ta gida. A nan ne na tattauna da ita a kan yadda take gudanar da wadannan ayyukan. A amsarta ne na fahimci cewa abin da ta dauka a rayuwar mace kawai shi ne ta haihu ta yi raino ta yi ayyukan gida, sai na nuna mata cewa ai duk da haka akwai abubuwan da ya kamata mu yi don inganta rayuwarmu a matsayinmu na mata.
Bayan na dawo sai wannan abu ya tsaya mini a rai, sai na yanke shawarar komawa wannan kauye don tattaunawa da matan kauyen kan abin da ya shafi inganta rayuwarsu. Sai dai abin takaici lokacin da na koma sai na samu labarin matar nan ta rasu wajen haihuwa. Wannan lamari ba karamin tsaya mini a rai ya yi ba. Daga nan sai na dauki aniyar shiga kauyuka don wayar da kan mata game da rayuwa gaba daya. A hankali-a-hankali sai abin ya zama kungiyar WOFAN. Da na tashi sanya tambarin kungiyar sai na sa hoton mace mai ciki da kaya a kanta da kuma dabbobi a gabanta, wato kwatankwacin matar nan da na gani a kauyen Ikara.
kungiyar WOFAN ba wai tana nufin ci gaban mata monama ta hanyar zuba taki a gona kawai ba, ya shafi batun iliminsu da lafiyarsu da ta ‘ya’yansu da kuma yadda za su samu kudin shiga da sauransu. Idan mun shiga kauyuka, mukan duba bukatun al’ummar wurin da farko, taimakon da za a bayar a wancan kauyen daban ne da na wani kauyen.
WOFAN takan taimaka wa mata a harkar noma da kuma sana’o’i, amma a kungiyance. Mukan koya musu yadda za su yi noman da kuma sarrafa amfanin gona har zuwa shigar da shi kasuwa. Duk abin da ake yi a WOFAN tsakanin ’yan kungiya ne, shi ya sa ba za ki ji rigimar kudi a wurinmmu ba, domin matan kowace kungiya za su zauna su zabi shugabanni a cikinsu da kuma yadda za su rika tara kudin kungiya don amfanin kansu. Idan muka horar da su sai yaye su domin su ci gaba da tafiyar da harkokinsu tare da kafa wasu kungiyoyi karkashinsu. Haka kuma muna da gona ta gwaji da muke ba manoma.
WOFAN tana samun kudin shigarta ne ta hanyar ayyukan da take gudanarwa amma ba daga kungiyoyin mata ba. Muna da sashen tuntuba inda manyan kungiyoyi na duniya ke ba mu aiki musamman da suka shafi yin bita. Haka muna gudanar da sana’oinmu da sunan WOFAN.
Abin da ke sanya ni farin ciki
Idan kin ji ni ina dariya to wallahi ina tare da ‘yan kungiya. Idan na shiga kauye nakan zauna cikin mata mu yi wasa da dariya a yi mai a ci kuli-kuli tare. Wannan abu yana faranta mini rai. Za ki je bukukuwa goma ko ashirin da wuya ki gan ni a wurin.
kalubale
Idan an yi batun nasara dole ne kuma a daya bangaren akwai kalubale. Mukan hadu da mutanen da ba su da hakuri wajen ganin an tafi da komai a hankali. Misali a yawancin lokuta mutane kan yi zaton cewa idan sun zo WOFAN kudi za su samu kai tsaye, wanda mu kuma a tsarinmu ba haka ba ne, domin mu ba mu son mu ba mutum kudi, mun fi so mu koya wa mutum yadda zai nemi kudinsa da kansa. Sai ki ga an wayi gari ire-iren wadancan mutane da suka shigo da wata manufa sun daina zuwa, saboda ba su samu abin da suke nema ba.
Kwalliya
Gaskiya ba na yin wata kwalliya da ake yayi. Ina kirkirar tawa daban, duk abin da ya kwanta mini a rai shi nake bi. Sai dai duk da haka ina damuwa da yanayin shiga cikin taro, wanda nake yi daidai da yadda ya dace da addini da kuma al’ada.
Abin da na fi sha’awar yi
Ina yawan motsa jiki, musamman a lokutan da na kebe ni kadai. Wannan motsa jikin ina ganin shi yake taimaka min wajen samun karfi, kasancewar na kai shekara 50 a duniya, amma har yanzu ina da karfin da nake gudanar da zirga-zirga ba tare da gajiya ba. Haka kuma ina son yin girki, domin a yanzu haka ni nake girka abincin gidana tun daga kan na maigidana har zuwa na masu gadin gidan. Ina son yin girki kwarai da gaske.
Yadda take hutawa
Ni tun ina karama ba ni da lokacin hutawa, domin ko a makaranta idan ana barcin rana, ni ba na iya yi. Sai dai fa ina da wani tsari idan na tashi daga aiki daga karfe shida, ba waya ba komai a gabana sai harkar iyalina. Daga nan kuma har na yi barci.
kasashen da na fi son ziyarta
Duk da cewa na ziyarci kasashe da dama a duniya, tun daga karatu zuwa harkokin kungiya, na fi son kasar Saudiyya saboda ibada, inda zan zauna na roki Allah gafarar kura-kurai da kuma neman biyan bukatu na Allah Ya inganta kungiya da kuma sauran al’umma gaba daya.
Abin da na fi so a tuna ni da shi
Batun taimakon mata, ina so a tuna ni a matsayin wacce ta inganta rayuwar mata. Misali ki samu wata mace ta ba ki labarin irin yadda take a baya, ga kuma ci gaban da ta samu a dalilin shigarta kungiya. Ina so a san ni a matsayin wacce ta ciyar da rayuwar al’umma gaba, amma ba wai abin da ya shafi ci gaban kaina ba.
Shawarata ga mata
Ina shawartar mata ‘yan uwana su mike tsaye su san cewa za su iya magance matsalolinsu da kansu. Haka kuma ya kamata su san cewa duk abin da wani ya yi su ma za su iya yi, abin da ake bukata kawai shi ne jajircewa. Lokaci ya wuce da mata za su kwanta su zuba wa mazajensu ido sai sun kawo sun ba su. Ya kamata su san cewa suna bukatar ingantacciyar rayuwa mai cike da lafiya da kuma ilimi, wannan kuwa ba su kadai ba har ‘ya’yansu.
Ina kuma kiran mazaje da su rika ba matansu goyon baya, domin bincike ya nuna cewa duk irin abin da mace ta zama a duniya iyalinta wanda mijinta yana daga ciki su ne mutane na farko da za su amfana da abin da ta samu.