✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajiya Safiya A. Umar Galadima: Mata a daina gulma

Hajiya Safiya A. Umar Galadima ‘yar gidan Galadiman Muri na II ce, ta yi gwargwarmaya wurin koyarwa, domin ita ce mace ta farko a jihar…

Hajiya Safiya Umar Galadima Hajiya Safiya A. Umar Galadima ‘yar gidan Galadiman Muri na II ce, ta yi gwargwarmaya wurin koyarwa, domin ita ce mace ta farko a jihar Taraba a matsayin baturiyar makaranta. Ta zama babbar mai kula da ilmi a ma’aikatar ilmi ta jiha, ta yi ritaya a matsayin darakta a hukumar. Ita ce Shugabar farko ta kungiyar Taimakon Mata ta kasa (NCWS), a yanzu haka kuma ma’aji da kuma Amira kungiyar FOMWAN, reshen Jihar Taraba. 

Tarihin rayuwata
Sunana Hajiya Safiya A. Umar Galadima, ’yar  Galadiman Muri na II, waton uban kasar Lau a da can baya, an haife ni a Kunini shekarar 1954, na yi firamare dina a Kunini 1960, daga nan na je makarantar horar da malamai da ke Maiduguri,  a nan na samu takardar malanta wato Grade II. Bayan na kammala sai na zama malamar makarantar firamare, na kuma yi aure, daga baya na ci gaba da karatuna a Jami’ar Bayero ta Kano, a nan na yi satifiket kan gudunarwa da tsare-tsare, baya nan sai Jami’ar Ahmadu Bello Zariya na yi Babbar Difloma kan harkar ilmi. Ina da ‘ya’ya shida, mata uku; maza uku, amma babbar ‘yata Zainabu Allah Ya yi mata rasuwa, wadanda suke raye yanzu akwai Muhammad Bello da Muhammad Nuru da Aishatu da Usman Shehu da kuma Farihatu.

Abin da ba zan taba mantawa da shi ba
Abin da ya fi burge ni wanda ba zan manta da shi ba shi ne, zuwana Hajji, domin kafin na je sai dai mu ji ko mu gani a talabijin, mun kuma karanta a littattafai a makaranta, amma da Allah Ya kai ni a shekarar 1983, sai na ce lallai Musulunci yana da dadi domin duk abin da muka karanta sai da muka gan shi wanda ya nuna ba karya a littattafanmu, ga shi muna cikin kuruciya muka yi aikin yadda ya kamata, kuma cikin ikon Allah ni na biya wa kaina wannan shi ne abin ba zan taba mantawa da shi a rayuwata ba.
Nasarori
Alhamdu Lillah, na samu nasarori da ban yi tsammani zan samu ba, a tsarin aiki na yi kansila ba tare da zabe ba umarni ne daga fadar Shugaban kasa, wato  a lokacin Janar Abaca. Bayan na kamamala wa’adin kansila sai na dawo kan aikina domin a lokacin ni ce Daraktar kula da aiki a ma’aikatar kula da makarantun firamare ta karamar hukuma, kafin wannan lokacin na yi malamar makaranta, sannan an nada ni shugabar makaranta. Ni ce shugabar makarantar G.R. A Yola, Jihar Adamawa ta farko, na kuma yi malama mai zagaye (bisiting teacher) duka a Yola, ina kan wannan kujera aka ba ni mataimakiyar sakataren ilmi ta II, ba da jimawa ba na zama ta I, ana haka sai na zama sakatariyar ilmi duk a Yola, daga nan na zama sakatariyar ma’aikatar da aka kirkiro da karamar hukumar Ardo-Kola, ni ce mace ta farko a jihar Taraba a matsayin Baturiyar makaranta. Sa’annan hukumar kula da ilmin  firamare ta jiha ta nada ni a matsayin jami’a mai kula da yanki wanda ya kunshi kananan hukumomi shida, bayan na zama babbar mai kula da ilmi a ma’aikatar ilmi ta jiha, na kuma rike mukamin mataimakiyar darakta a hukumar, na bar aikin gwamnati a matsayin darakta. Duk da haka ban koma gida na zauna ba, na ci gaba da aikin taimakon jama’a inda na zama shugabar farko ta kungiyar taimakon mata ta kasa (NCWS), sannan mamba a kungiyar Jama’atu Nasril Islam, yanzu haka ni ce  ma’aji da Amira ta FOMWAN, reshen Jihar Taraba. A sauran ayyukan sa kai kuwa na rike matsayin shugaba a dandalin siyasa na jiha kuma mamba a kungiyar mata wadda matar Gwamnan Taraba ta kafa wato (Better life,) na rike shugabar mazaba ta hukumar zabe, na shugabanci kungiyar mata, reshen Jihar Taraba, bayan kungiyar zawarawa da marayu da NASFAT ina cikin kungiyoyi fiye da goma.

kalubale    
Da ma a kullum ba zai yiwu a ce komai kake yi kana jin dadi ba, dole ka fuskanci matsaloli, ta yaya za ka fuskanci al’amarin, to Alhamdu lillah da hadin kan mahaifana da ‘yan uwana da masoyana duk kalubalen da na fuskanta bai zame mini barazana ba wurin hana cin nasarata. Sai dai a yanzu ina fuskantar matsalar rashin kudi na gudanar da ayyukan da muka sa gaba na kungiya, duk da wasu na taimakawa amma har yanzu muna da bukatar a wuce haka kamar gyara mana makaranta da wasu suka yi ta ALkALAM. Da yawa akwai abin da kake tunani amma wani ba shi yake tunani ba, wannan kan kawo mana matsala.
Lambobin yabo
Alhamdu lillah, na samu lambar yabo daga kungiyoyi masu yawa, na farko, kungiyar matasa masu neman ci gaban Jihar  Taraba. kungiyar daliban Jihar Taraba ma sun ba ni kan yadda nake taimaka musu, kungiyar Malamai ta Jiha (NUT) ma ta ba ni lambar yabo, kungiyar Matan Arewa sun ba ni kyauta a matsayin jakadiyar Arewa, kungiyar Muryar Talaka sun ba ni lambar yabo a Kaduna. kungiyar Matan Najeriya sun ba ni lambar yabo kan kwazon aiki har guda biyu, daya a Jihar Yobe; daya kuma a Jihar Imo, Kungiyar Mata Musulmi reshen jiharmy ta karamma ni. Wadannan ne kadai nake iya tunawa.
Tafiye-tafiye
Na je Saudiya Arebiya da Turkiyya da Italiya (Rum), na je kasashe da yawa, amma a nan Najeriya Jihar Ikiti ce kadai ban je ba.
Abin da ya fi burge ni
Abin da ya fi burge ni a rayuwa shi ne samun haihuwa, don ba kowa ne zai samu da ba, a lokacin da na samu haihuwar farko na yi farin ciki fiye da yadda kake zato, don na rika ganin kaina kamar ni kadai ce ke da ‘ya a duniya. Allah Ya azurta min ita da son addini da iyaye kuma ita ce wacce ba ta jima ba, ta rasu ne a lokacin da ta zo haihuwa. Abu na biyu da ke ba ni sha’awa shi ne ka ga abokan zaman suna zaman lafiya ba wata hayaniya, ana ta dariya da annashuwa da yin kalamai masu ma’ana, idan na ga wadannan mutane nakan zauna kusa da su saboda sha’awar da nake da ita kansu.
Abin da na fi so a rayuwa
Na fi son lafiyar kaina don taimaka wa addinina, na ba ‘ya’yana tarbiyya, su dogara da kansu shi ne na fi so a rayuwata.
Burina
Buri na in na mutu in shiga Aljanna, domin wannan rayuwar duk wanda ya mutu bai shiga aljanna ba ya yi hasara. Burina biyu shi ne in ga Manjo Al-Musatafa a fili yana yawo kamar kowa kuma a ranar uku ga watan Ramadan na ji dadi fiye da yadda kake zato da aka saki shi, kuma bai san ni ba amma ina tausaya masa ne kamar dan da na haifa.
Kirana ga mata
Ina rokon mata ‘yan uwana su sanya hankalinsu a jikinsu, wadanda ba su yi aure ba su san Allah ne ke yi don kada su je su sabi Allah, don kawai neman yin aure, kuma su rika yin ado irin na Musulma sabanin haka ba su kyautata wa musulunci ba. Wadanda suka yi auren kuwa su rike auren tsakani da Allah duk abin da miji ke musu kada su damu domin bautawa Allah ne suke yi, su san akwai ranar da wani zai nemi wani amma ba zai gan shi ba. A yi hakuri da auratayya da abin da aka haifa, sa’annan mata su rage gulma da hada fada tsakanin ma’aurata, kannen miji su tsaya matsayinsu, iyaye ma haka, ku bari ‘ya’yanku su ji dadin aurensu.