Hajiya Sa’a Ibrahim ’yar jarida ce wadda ta shafe shekaru sama da ashirin tana gudanar da aikin a gidajen rediyo da na talabijin da ke Kano.Haka kuma ta yi aiki a gidan rediyon Muryar Jamus. A yanzu haka ita ce Shugabar Gidan Talabijin na Abubakar Rimi da ke Kano.
Tarihin rayuwata
An haife ni a unguwar Magashi cikin Jihar Kano. Sunan mahaifina Ibrahim Bello ya yi aikin gwamnati a ma’aikatar noma. Na yi karatun firamare a makarantar firamaren kofar Kudu ta cikin gidan sarki. Bayan na kamalla sai na shiga makarantar sakandiren ’yan mata ta Dala. Bayan na kamalla sai na tafi Kwalejin Share Fagen shiga Jami’a (CAS) daga nan na sami shiga Jami’ar Usman danfodiyo, da ke Sakkwato. Bayan na kammala a shekarar sai na je na yi hidimar kasa a Jihar . Bayan na gama a shekarar 1984 sai na sami aiki a gidan rediyon Kano. Kasancewar ba fannin aikin jarida na karanta ba a shekarar 1985 sai na ga dacewar na sami karin karatu a fannin aikin da na sami kaina a cikinsa, don haka sai na tafi Jami’ar Jos na yi babbar difuloma a fannin shirye-shiryen rediyo . A shekarar 1986 sai gidan rediyon Jamus ya zo yana neman ma’aikata don haka na tafi can na yi shekara biyu. Bayan na dawo sai na koma na ci gaba da aikina a gidan rediyo inda na tarar an bude bangaren FM, don haka sai aka tura ni can inda muka ci gaba da watsa shirye-shiryenmu cikin harshen Turanci. Ina nan a wannan bangaren sai na sake komawa
Jamus na yi shekara uku zuwa hudu. Da na dawo ma gidan rediyon na ci gaba da aikina. Kasancewar a wancan lokaci gidan rediyo da na talabijin na Jiha suna karkashin hukuma daya ne sai a shekarar 1996 aka mayar da ni aiki a wannan gidan talabijin na Abubakar Rimi(ARTb) a matsayin Manaja ta shirye-shirye. Babu shakka na ji dadin aikina a wanann wuri kasancewar an ba ni aiyukan da nake so, wanda suka sa na zama cikin aiki ko da yaushe. Ina iya tunawa a lokacin ni ce nake gabatar da shirin mata na Turanci da Hausa da shirin yara na Hausa da na Turanci. Ina nan ina aikina zuwa wasu shekaru sai aka raba gidan rediyo da na talabijin aka mayar da ko wanne a matsayin hukuma mai cin gashin kanta. Hakan ya sa na koma wurin aikina, wato gidan rediyo. Na ci gaba da aikina har zuwa wannan lokacin da Gwamnan Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso a shekarar bara 2014 ya dauko ni ya ba ni shugabancin wannan wuri.
Nasarorin da na samu
Alhamdulillahi,na samu nasarori masu tarin yawa a harkar aikina na jarida. Nakan gaya wa yaran baya masu tasowa cewa aikin jarida, aiki ne da yake bukatar jajircewa, kasancewar aiki ne da yake bukatar zirga-zirga da tafiye-tafiye. Babu shakka nasarar da na samu ta samu ne dalilin hadin kan da na samu daga mahaifina kasancewarsa mutum mai son karatu da aiki. Haka kuma bayan na yi aure na sami goyon baya daga maigidana. Abu na biyu shi ne a harkar aikina nakan nemi taimakon duk wanda ya cancanta ya taimaka min ba tare da girman kai ba. Har ila yau kuma nakan ja ma’aikatan da suke karkashina jikina don samun tafiyar da aiki cikin nasara. Lokacin ina aiki a FM na dace da samun abokan aiki da muka tsaya muka gudanar da aiki cikin nasara. Tun daga lokacin da Mai girma Gwamna ya dauko ni ya damka min ragamar shugabancin gidan nan sakamakon tabarbarewa da al’amuran gidan ya yi muka zo muka fara aiki muka fara samun nasara. Lokacin da na zo gidan talabijin din nan babu wasu kayattatun shirye -shirye da ake sanyawa. Yawancin tsofaffin shirye-shirye ne ake saka wa, wanda ana kallo suna rawa. Haka kuma ana bude tashar ne da yamma misalin karfe biyar na yamma sannan a rufe misalign karfe 11:00. Amma a yanzu cikin ikon Allah mukan bude tasharmu a ranar Litinin zuwa Juma’a daga karfe 11na rana sannan mu rufe da misalign karfe 12:00. Haka kuma a ranakun karshen mako mukan bude tun daga karfe 8:00 na safe zuwa 12:00 na dare. Sannan kuma muna kokarin samar da sababbin shirye-shirye masu gamsarwa. Har ila yau mukan yi kokarin hawa kan tsarin Startimes don jama’a su sami sauki wajen kama tashoshin gidan talabijn na Abubakar Rimi. Ga shi kuma ana kama mu a tashar rediyo ta Fm.
Mun gode Allah da kuma Gwamna bisa ba mu dama da kuma kayan aiki da ya yi, domin duk iya aikinka idan ba ka sami kayan aiki ba, to aikin ba zai yiwu ba. Alhamdulillahi kullum sai yabo muke samu daga jama’a game da yadda aiyukan wannan gidan talabijin yake tafiya a yanzu.
Alhamdulillah zan yi amfani da wannan dama wajen godiya ga ‘yan uwa da abokan arziki bisa addu’a da taimako da suke ba mu wajen tafiyar da aikin nan.
kalubalen da na fuskanta
Duk da cewa babu wani aiki da mutum zai yi ba tare da ya samu matsala ba, a gaskiya ni dai matsalolin da na fuskanta a harkar aiki kalilan ne .Wannan kuwa ya samu ne sanadiyyar riko da gaskiya da na yi wa aikin da kuma jajircewa wajen tafiyar da shi. Ni mutum ce mai son aikina kwarai da gaske. Ba karamar rashin lafiya ce take hana ni zuwa wajen aiki ba . Allah-Allah nake gari ya waye na tafi wurin aikina. Wani lokaci ina kan tebur dina mai sharar ofis dina zai zo ya same ni.Dole idan mace tana aikin jarida sai ta sami cikakken goyon bayan mijinta, idan ba haka ba kuwa to aikin ba zai yiwu yadda ake bukata ba. A yanzu idan aiki ya dauro sai mu kai karfe goma sha biyu na dare a ofis muna aiki, kin ga wannan idan ba kyakkyawar fahimta kin ga sai a sami matsala a gida. Haka kuma ba na mantawa na haifi dana na fari ko arba’in ba mu yi ba muka tafi aiki Jihar Neja.kalubalen da nake ganin na hadu da shi zai iya zama na wata rana da muka je aiki Jihar Yobe barayi suka tare direbanmu aka kwace masa mota, mu ma kanmu da kyar muka tsira.
Iyali
Bayan na dawo daga Jamus na yi aure. A yanzu haka ina da ‘ya’ya biyu maza. Babban ya kammala karatunsa na digiri har ma yana aiki. Sai na biyun yana gab da shiga Jami’a.
Burina a rayuwa
Babban burina shi ne na samu na cika da imani. Sannan kuma ina matukar kaunar cewa na ga na taimaka wa wanda ya zo neman taimako gurina. Ba na kaunar na ga wani na kusa da ni a cikin matsala ba tare da na yi kokarin fitar da shi daga cikin matsalar ba. Ina da burin yau a ce na
sami damar da zan yi wani abu da zai zama sanadiyyar ci gaban jama’a a matsayin tawa gudummawar in sha Allah. A harkar aiki kuma ina burin na ga an ba ni aikin da tunanina zai iya,
na samu na aiwatar da shi kamar yadda ake bukata. Burina a yanzu shi ne na ga gidan talabijin na Abubakar Rimi ya kai matsayin da duniya ma ta san da zamansa ba wai kawai a cikin kasar nan ba. A yanzu muna kan hanyar samun hakan in sha Allah kasancewar Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da kwangilar daga darajar gidan wannan talbijin yadda zai yi kafada-da- kafada da takwarorinsa na duniya.
Abin da nake so a tunani da shi
Zan so a tuna da ni a matsayin wadda ta taimaki jama’a ta hanyoyi da dama, da kudinta da shawarwari da sauransu. A kullum idan na sami naira dubu, na fi sha’awar na kashe naira dari bakwai ta hanyar taimakon jama’a.
Shawara ga mata
Shawarata ga mata ita ce su tashi su nemi ilimin addini da na zamani,idan mace na da ilimi takan sami damar gudanar da rayuwarta yadda ya kamata. Daga irin tambayoyin da ake aiko wa malamai za ka ji yadda wasu matan suke zaune a cikin gidajensu, aurensu ya lalace amma saboda rashin ilimin addini sai su ci gaba da zama a hakan, saboda a ganinsu zaman a hakan ya fiye musu rufin asiri. Sannan akwai bukatar mata su nemi sana’a yadda za su dogara da kansu. Ba sai mace ta fita ta yi aiki a waje ba, akwai sana’o’i birjik da za ta iya gudanarwa a cikin gidanta. A da idan mijin mace ya mutu ‘yan uwansa ne ke daukar nauyin’ya’yan da ya bari, amma yanzu saboda halin da aka shiga na matsin rayuwa babu wanda ke daukar ’ya’yan sai dai a bar mace da wahalar ’ya’yanta, to a irin wannan yanayi ta yaya za ki iya daukar nauyin rayuwarki da ta ’ya’yan ba tare da kina da abin yi ba. Sannan kuma ina shawartarsu da su rike duk wani abu da suke yi da muhimmanci, wannan ya hada da aiki ko kasuwanci , duk abin da mutum ya yi wasarere da shi to daga nan ne ake samun matsala.