✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajiya Hajarat danyaro Ibrahim: Burina in taimaki nakasassu

Hajiya Hajarat danyaro Ibrahim ita ce  mai ba Gwamnan Jihar Nasarawa Alhaji Tanko Al-Makura shawara kan harkokin siyasa, kuma daraktar kungiyar wayar da kai ta…

Hajiya Hajarat danyaro Ibrahim ita ce  mai ba Gwamnan Jihar Nasarawa Alhaji Tanko Al-Makura shawara kan harkokin siyasa, kuma daraktar kungiyar wayar da kai ta TA’AL. ’Yar siyasa ce, tana kuma kasuwanci. Ta ce burinta ta taimaki nakasassu, sannan a tuna ta a matsayin matar da ta sadaukar da rayuwarta wurin taimaka wa al’umma.
Tarihin rayuwata
Sunana Hajiya Hajarat danyaro Ibrahim. Ina da aure da ‘ya’ya 5, kuma ni ce Daraktar wayar da kan matan kungiyar TA’AL a Lafiya da ke Jihar Nasarawa. Kuma ni mamba ce a kungiyar Task Force da Maigirma Gwamnan Jihar Nasarawa ya kirkiro a jihar a shekara 2011. Ni ce kuma shugabar cibiyar yaki da jahilci a Jihar Nasarawa. Na yi kwamishina a Hukumar gudanar da zabubbuka a Jihar Nasarawa daga shekara 2000 zuwa 2005. Na kasance mace ta farko mai ba gwamna shawara kan harkokin jam’iyyun siyasa daga shekara ta 2012 zuwa yau. Ina da babbar Difloma a fannin Ilimi daga jami’ar koyar da malamai a Kaduna da yanzu aka hada ta da Jami’ar Usman danfodiyo da ke Sakkwato. A halin yanzu dai bayan aiki da nake yi ina kuma karatun digiri-na-biyu a fannin kasuwanci a jami’ar Jihar Nasarawa da ke garin Keffi.    
Burina lokacin da nake karama
Burina lokacin da nake karama shi ne, idan na girma na zama malamar lafiya. To amma Allah bai nufa haka ba. Sai na zama ’yar kasuwa kuma ’yar siyasa, saboda a lokacin na yi burin zuwa jami’a don na karanci fannin magunguna, sai mahaifina a lokacin ya ce tun da an bude makarantar kimiya da fasaha ta tarayya a garin Nasarawa sai na yi karatu a gida, daga nan sai ya tura ni wannan makaranta, inda na karanta fannin harkokin kasuwanci.
Abubuwan da na koya daga iyayena
Na koyi abubuwa da dama daga wurin iyayena.  Idan na ce zan bayyana abubuwan da na koya sai mu kwana ban gama ba, amma zan fada maka kalilan daga ciki. Na koyi girmama na gaba da ni. Na biyu kuma, na koyi in kasance mai godiya ga abin da Allah Ya ba ni, saboda na tashi na tarar da mahaifina attajiri ne, wanda a lokacin a garinmu babu mai arzikinsa. Amma daga baya aka wayi gari sai muka ga wasu sun zo sun dara mu. Amma wannan bai birkita mahaifina ba, bai kuma canja rayuwarsa ba, ya zamanto mai godiya ga duk abin da Allah Ya yi masa a kodayaushe. To, ni ma sai na yi koyi da wannan halin, wato wadatar zuci. Na kasance mai gode wa Allah a duk halin da na samu kaina a ciki. Na koyi wannan daga wurin iyayena ne musamman mahaifina.
Burina
Burina a yanzu shi ne na taimaki nakasassu, ya kasance idan an ambace ni su tabbatar da na taka muhimmiyar rawa a rayuwarsu.
Yadda nake lura da iyayena
Ina da mahaifa; ga ‘ya’ya; ga miji. A halin yanzu ina da ‘ya’ya biyar. Biyu na karatu a jami’a, sauran kuma suna kananan makarantu. Nakan yi kokarin rarraba lokutana don na ga cewa kowanne a cikinsu ya samu lokaci da ya kamata ina ba shi.  Nakan bambanta lokacina ta yadda dukkansu za su samu kulawata.
kalubalen da na fuskanta a rayuwata
Babu wanda zai gudanar da rayuwarsa ta yau da kullum ba tare da ya fuskanci kalubale ba. Na fuskanci kalubale, sai dai yawancin kalubalan da kusan dukanmu mata muke fuskanta shi ne, maza na yi mana kallon raini, ko ba za mu iya ba. Za ka samu idan abu ya taso kuma akwai namiji da kuma mace, sai a rika ganin ai mace ba za ta iya ba, amma idan aka ba mu damar aiwatarwa sai ka ga mun yi fiye da abin da namiji zai yi, a kullum hakan na ci mini tuwo a kwarya.
Yadda na magance kalubalen da na fuskanta
Da zarar na aiwatar da wannan aiki da namiji ke ganin kamar ba zan iya ba a matsayina na mace, sai ka ga na kasance cikin jin dadi da farin ciki, kuma hakan na nuna musu fa mata ma ba baya ba ne.
Nasarar da na cim ma
To, Alhamdu Lillah, na gode wa Ubangiji da Ya yi ni mace, Ya kuma yi ni Musulma, Ya kuma fara ba ni shugabanci tun ina yarinya, domin na fara rike shugabanci a rayuwata tun ban wuce shekara 13 ba, wanda idan ka duba a tarihin da na ba ka a baya, na fara rike shugabanci ne na kungiyar kwallon kafa ta mata, wanda kuma kowa ya san maza ne da harkar kwallo. Na sake zama shugabar mata masu kidan shantu. A wannan lokacin duk da karancin shekaruna na kasance mace ta farko da ta fara rike wannan matsayi, inda ina koya wa yara yadda ake kida da shantu. To, ka ga shi kansa wani abu ne babba a rayuwa da har yanzu nake alfahari da shi, wanda kuma a yanzu gani na kai wannan matsayi. Na samu nasarori a rayuwata.
Wuraren da nake sha’awar zuwa lokacin hutu
Wuraren da nake sha’awar zuwa lokacin hutu na su ne, wuraren wasan motsa jiki musamman wasan Jim. Na kasance mai son wasan motsa jiki, saboda ko a lokacin da nake matashiya ina son wannan wasa. Tun ina makarantar sakandare nake yin gudu ina buga kwallon kwando (Basket ball), duk a lokacin kuma nakan yi tsalle-tsalle da sauransu. Kodayake yanzu ba zan iya yinsu sosai ba, amma har yanzu ina cikin masu son wadannan wasanni da na bayyana musamman lokacin hutuna.
Abin da nake so a tunani da shi
Abin da nake so a tuna ni da shi bayan ba na nan su ne, kauna da kulawa da kuma taimaka wa nakasassu cikin al’umma.
Tallafi daga maigidana
A hakikanin gaskiya ina samun goyon baya sosai daga wurin maigidana. Duk abubuwan da na bayyana maka ba don na samu goyon bayansa ba da ban kai ga wadannan nasarorin da na cim ma ba. Maigidana ya kasance mutum ne mai ba ni kwarin gwiwa a duk harkokin da na sanya a gaba, shi ya sa nake samun nasara. A duk lokacin da na samu karaya, ina ganin ba zan iya ba yakan ba ni karfin gwiwa. Yakan ce mini: “Za ki iya, ki tuna a baya kin yi kaza lokaci kaza, kuma kin yi nasara. Ki sanya a ranki za ki yi nasara wannan karon ma.’’ Saboda haka a kowane lokaci yakan kasance mai ba ni goyon baya da karfafa mini gwiwa.
Babbar kyauta daga maigidana
Ba zan iya tunawa da babbar kyauta da maigidana ya taba ba ni ba, kasancewar sau da yawa yakan ba ni kyaututtuka daban-daban. Ba zan iya tuna wacce ta fi girma cikinsu ba.
Abin da nake sha’awa cikin kayan koli
Abubuwan da na fi sha’awa a kayan koli su ne, gazal da Jan-baki, saboda ni mace ce wadda idan na wayi gari ban sanya jan-baki a lokacin da nake kwalliya ba sai in ji kamar ba ni da lafiya.
Halayen da nake sha’awa wurin mata
To, a cikin halayen mata wanda na fi sha’awa shi ne, in ga mace mai fara’a wadda a kowane lokaci za ka tarar da ita cikin yanayi na farin ciki. A duk lokacin da ka zo gare ta ko ta sanka ko ba ta san ka ba za ta karbe ka da hannu biyu da kuma murmushi. Hakan na ba ni sha’awa cikin halayen mata. Kowane lokaci tana cikin halin walwala ba kunci.  Shi ya sa a duk lokacin da mutum ya zo wurina ko na san shi ko ba san shi ba, nakan karbe shi da hannu biyu cikin fara’a da murmushi.
Turaren da na fi sha’awa
Na kasance ina da yawan son turare amma yawancin turare da nake amfani da su turare ne na Larabawa, wato Arabian perfume ke nan a turance.
Tufafin da na fi so
E to, tufafin da na fi so shi ne, irin namu na ‘yan Afirka da kuma irin na matan Arewa, shi ya sa sau da yawa za a gan ni cikin atamfa ko kuma shadda.