✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajiya Hadiza Ladi Abdullahi: Burina in taimaka wa mata

su tsaya da kafafunsu. Hajiya Hadiza Ladi Abdullahi ita ce Kwamishinar Ma’aikatar Kula da Albarkatun Ruwa a Jihar Neja, kuma jagorar kungiyar Taimakon Marasa Galihu…

su tsaya da kafafunsu.

Hajiya Hadiza Ladi Abdullahi ita ce Kwamishinar Ma’aikatar Kula da Albarkatun Ruwa a Jihar Neja, kuma jagorar kungiyar Taimakon Marasa Galihu (Educationally Challenged, Handicapped and Orphans Foundation (ECHO). Burinta ta taimaka wa mata har su tsaya da kafafunsu.

Tarihin rayuwarta
Sunana Hajiya Hadiza Ladi Abdullahi Kwamishinar Ma’aikatar Kula da Albarkatun Ruwa  ta Jihar Neja, an haife ni a Zariya a watan Afrilun shekarar 1960. Yanzu ina da shekara 53 da ‘yan watanni. Na girma a Minna, kuma ni ‘yar hedikwatar karamar Hukumar Chanchaga ce. Na yi firamare, daga nan sai Kwalejin Koyar da Malanta ta ‘Yan mata da ke Minna (Women Teachers College), daga bisani na je Makarantar Share fagen shiga Jami’ar Ahmadu Bello a shekarar 1977. Da na samu nasara ne aka ba ni damar karanta kwas din Kimiyyar Siyasa, inda na kammala a 1981. Cikin  shekarar 1982 na yi hidimar kasa a Jaji da ke Jihar Kaduna.
Na fara aiki a Abuja, daga bisani aure ya mayar da ni Kano, inda na yi aiki da Kamfanin Jaridar Triumph da ke Kano shekara bakwai a matsayina ‘yar rahoto. Na sake koma wa Abuja sakamakon mayar da maigidana da aka yi zuwa can, inda kuma aka ba ni matsayin Shugabar Yanki na Jaridar Triumph a Abuja (Abuja Bureau Chief), na yi aiki a Majalisar da ta tabbatar da sake mayar da mulki hannun farar hula (Constituent Assembly). Daga baya na yi aiki da Hukumar Gudanarwa ta Babbar Birnin Tarayya (Federal Capital Territory Debelopment Authority). Na rike mukamai da yawa a hukumar har na kai matsayin Darakta, na kuma yi ritaya a shekarar 2009.
Babban dalilin da ya sa na yi ritaya shi ne don na gudanar da ayyukan lada da kuma koyar da jama’a. Babban burina ina karama shi ne, in zama malamar makaranta. Wannan ne ya sa na kafa kungiyar Taimaka wa Marasa Galihu. Da Gwamna ya ji na yi riyata sai ya kira ni in yi masa aiki a Hukumar Kare Muhalli ta Jihar Neja (Niger State Enbiromental Protection Agency), a yanzu kuma kwamashinar kula da albarkatun ruwa.
kalubalen da na fuskanta lokacin neman ilimi
Mu takwas ne a wurin mahaifiyarmu; biyar mata. Ni ce ta biyu. A lokacin mahaifina ba shi da abun hannu, saboda wadansu kalubale na rayuwa, mahaifiyarmu kuwa mace ce wadda ta yarda da abu mai inganci duk in da yake, muddin za a same shi. Don haka ne ta bugi kirjin sai yayarmu Rakiya ta shiga makarantar Fatima Secondary School, domin kuwa abin alfahari ne a ce ‘ya’yan mutum suna wannan makarantar. Kudin makarantar fam 42 ne. Samun wannan kudin a wasu lokuta sai an sayar da wadansu kayayyaki. Bayan an biya mata kudin kuma ni kuma babu wanda za a biya mini nawa.
Ana cikin haka ne, gwamnati ta bude makarantar malanta ta mata (Women Teachers College)  da iyaye da dama suka samu damar tura ‘ya’yansu can, inda aka rika ba mu kayan makaranta kyauta. Talata da Laraba ana ba mu gyada da madara. A lokacin ana koyarwa yadda ta kamata, kusan babu bambanci tsakanin makarantun gwamnati da na masu zaman kansu. Bambancin dai, na gwamnati ba a biya. A lokacin da muke makarantar, akwai wadanda aka ba izini suka yi aure, sannan aka ba su hutun shekara. Wannan matakin ya ba ‘yan mata da dama damar karatu daga birane da yankunan karkara.
Dalilin da na kafa kungiyar taimakon marasa galihu
Bayan na dawo gida ne fara mu’amala da ‘yan siyasa, wanda hakan ya tilasta mini hulda da jama’a fiye da yadda na saba. A nan na kara gane gwagwarmayar da mata ke yi a harkokin rayuwar yau da kullum musamman ga iyalinsu.
Babban dalilin kafa wannan kungiyar shi ne, in taimaka wa iyayen da ke sha’awar ilimantar da ‘ya’yansu kuma ba su da hali.
A lokacin da nake Abuja na yi aiki tare da nakasassu, shi ya sa  na lashi takobin taimaka musu su don su cim ma burinsu a rayuwa. Ilimi shi ne babban makamin yaki da fatara da kuma jahilci. Na fahimci yawancin iyayenmu na fama da karyewar jarin sana’o’insu.
Na fara ne da taimaka wa wadanda suka cancanta da kudin da ya kama daga dubu 20 zuwa 30. Abin mamaki shi ne, wata in ka ba ta dubu 20 sai ta ce maka dubu 10 ya ishe ta juyawa. Wannan kudin da aka ba su ba kyauta ba ne, za su biya babu karin ko sisi. A duk sati wadda aka ba kudin za ta rika biyan naira dubu daya a hankali babu fashi, har sai ta gama biya. Ba za ta kara kwabo a kai ba. Ina da ma’aikatan da na dauka wadanda suke gudanar mini da wannan harkar duk wata ina biyansu albashi. Wannan ya bayar da dama wurin hada kan mata wuri daya suna gudanar da harkokinsu. Maza wadanda suka ci moriyar shirin da ma wadanda ba su ci ba, sun yaba sosai.
Bayan haka, mukan gudanar da darussa ga daliban da za su sake rubuta jarabawar kammala makarantar sakandare. Mun biya wa wasu daga ciki kudin rubuta jarabawar. Sannan muna yi wa wasu daga cikin matasan da ke neman kangare wa iyayensu nasihar dan abin da Allah Ya hore mana na Al-Kur’ani Mai Girma da Hadisan Annabi Muhammad (SAW) domin su bar wadannan miyagun dabi’un da suka hada da rashin da’a da shaye-shayen kwayoyi.
Yadda nake jajircewa don na ga an ci moriyar shirin
In kana neman wanda zai yi maka aiki yadda kake so, to ka nemi mace. Ka san duk abin da aka ce maka na mutum ne, ya fi sa masa ido sosai domin kwalliya ta biya kudin sabulu. Ita Kodinetan kungiyar ke rarraba takardun neman lamunin, don duk wanda ya zo wurina ma ba zan saurare shi ba. Duk wanda ya nemi a shiga unguwarsa kan shirya ne mu je a yi hira da mata, sannan mu yi musu bayanin shirin dalla-dalla tare da sharuddan da ke tattare da hakan. A nan sai mu nemi mata 10 masu sana’o’in da jarinsu ya karye da za mu fara da su a lokaci daya. Wadannan 10 da suka cancanta, sai a raba musu baki daya dubu dari 2 wato kowacce dubu 20 ke nan.
Mukan ba su tazarar mako biyu kafin su fara biyan naira dubu duk sati. Su wadannan matan ne za su bayar da rana da lokaci da wurin da za a hadu domin a karbi kudin bisa alkawari, ko da ba su cika ba, wadanda suka hadu ne za su bayar da na wadanda ba su zo ba. Wannan ne ya sa ko da mace ba za ta samu damar zuwa ba ta kan aiko da kudinta na ka’ida. Idan muka je karbar kudin, mukan tambaye su kalubalen da suke fama da su, ta haka sai mu ba su shawarwarin da za su taimaka musu, sannan mu sanar da su wasu shirye-shirye da manufofin Gwamnati, misali, muhimmancin iyaye su rika barin ana yi wa ‘ya’yansu allurar riga-kafi. Idan muka samu labarin cewar akwai matsala tsakanin mata da miji, mukan sasanta lamari.

Yawan matan da suka ci moriyar shirin
A bara cikin watan Yuni muka kaddamar da shirin, muka dan yi hutu kadan cikin watan Disamba, a wannan lokacin kimanin mata 250 ne suka ci moriya. A watan Janairun bana ne muka ci gaba da gudanar da harkokinmu. Babban burina a bana, shi ne, in ninka yawan wadanda suka ci moriyar shirin su kai 500 ko su zarta haka.
kalubale wurin gudanar da harkokina
Ba zan boye maka ba, wannan matsayin da na samu kaina na uwa, sannan kwamishina, ga kuma wannan kungiya, duk ba wasa ba ne. Sai dai duk abin da nake yi ina mika al’amurra na ne ga Allah (SWT) domin Ya zame mini jagora. A duk lokacin da na yi haka, ina samun saukin gudanar da su don kuwa wani lokaci nakan yi mamakin yadda muka samu wasu nasarorin. Ina raba lokutana ne. Iyali na sun san da haka kwarai da gaske.
Abinci da kuma lokacin hutu
A duk lokacin da na samu hutu, ina tare da iyalina, musamman ‘ya’yana kanana, ina shiga cikinsu mu yi ta labarai. Abu daya da kan faranta musu rai shi ne, na kan ce musu yau ni zan girka abincin gidan don haka kowa ya sa mini ido. Wani lokaci idan ina bukatar kadaici, nakan sanar da su don in yi abin da nake bukata.
Ga bangaren abinci ina sha’awar miyar kuka da taushe da kuma ta kubewa. Ina sha’awar tuwon shinkafa da na alkama da sakwara. Dangane da abun sha kuwa ina matukar son kunu tsamiya da na gyada da kunun zaki da zobo da kuma kunun aya.
Littafin da na fi son karantawa
 Na fi son karanta al-kur’ani mai Girma, musamman ta na’urar kwamfyuta, na kuma fi son in koyi harshen larabci. A wannan gabar nake fama kuma nake son Allah Ya cika mini burina. Ka ga muddin na iya larabci gwargwadon iko, zai kara mini fahimta ga fannin neman ilimi.
kasashen da na ziyarta
Na ziyarci kasashen da suka hada da Singapore da Sin (China) da Malesiya da Dubai wato Hadaddiyar Daular Larabawa, sai Faransa da Ghana da Jamhuriyyar Benin, sai kuma babbarsu gaba daya Saudi Arebiya. Ka san abin dariya ne wallahi ban taba zuwa kasar Amurka ba.
Shawara ga iyaye
Ya kamata iyaye su rika ilmantar da’ya’yansu ilimin addini da na boko. Su sa ido a kan ‘ya’yansu don su samu tarbiyya tagari har su zama abin alfahari ga al’umma.
Fatana
Wallahi ina fatan in gama da duniya lafiya, ina kuma fatan in zama mai godiya ga Mahaliccina a kowane hali, ina kuma fatan na samu kyakkyawar shaida, na zama abar alfahari ga kowa ba tare da la’akari da bambancin addini ko kabila ba.