Hajiya Bilkisu Wada ’yar siyasa ce da ta yi suna a jam’iyyar APC a Jihar Legas. Ta taba rike mukamin Shugabar mata ta jam’iyyar, kuma tana daya daga cikin jagororin mata ’yan Arewa a jam’iyyar. Bayan harkar siyasa Hajiya Bilkisu gawurtacciyar ’yar kasuwa ce da ke sayar da gwala-gwalai da atamfa da sauransu. Ta shaida wa wakilinmu irin gwagwarmayar da ta sha da kuma yadda take tafiyar da harkar siyasa da kasuwanci da kuma kula da iyali. Ga yadda hirar ta kasance:
Tarihin Rayuwata
To ni dai asalinmu ’yan jihar Gombe ne, amma ni an haife ni a cikin birnin Ikko fiye da shekara 50 da ta gabata. Na fara makaranta a Jihar Legas, daga bisani aka mayar da ni garinmu Gombe, inda na kammala karatuna na sakandire. Na yi aure a Jihar Legas da maigidana Wada. A yanzu na haifi ’ya’ya biyar tare da shi, daga bisani Allah Ya yi masa rasuwa. Allah Ya jikansa, amin.
Sana’a kafin harkar siyasa
Da farko kasuwanci nake yi. Na fara harkar sayar da gwal da zinare, daga bisani saboda yanayin kasuwa musammam ma bashi da ya yi yawa sai na koma sayar da kayayyaki kamar su atamfa da mayafi da takalma. Kuma ina sayar da lemon kwalba da makamantansu. Har yanzu nakan sari kaya daga wadanda suka sayo daga wasu wurare ni ma na sayar. Daga nan na tsunduma cikin kungiyoyin mata daban-daban inda na yi jagoranci a matakai iri-iri.
Gwagwarmar siyasa
Na fara siyasa tun zamanin Shagari. Da na yi aure sai na dakata amma bayan rasuwar maigidana sai na koma siyasa inda na shiga jam’iyyar AD, daga baya ta koma AC, aka sake canza mata suna zuwa ACN, sannan yanzu ta koma APC. Da mu aka rika yin gwagwarmaya har jam’iyyar ta samu kafuwa ta kuma karbu a wurin jama’a. Na shiga siyasa ne don kwato wa mata ’yanci, in tabbatar da cewa mata sun yaki talauci da jahilci sun dogara da kansu. Musamman matanmu na Arewa da ke yankin Surulere da Jihar Legas baki daya. Ina so a rika damawa da su, ana ba su dama don su ma su bayar da gudunmawarsu ga ci gaban Jihar Legas da kasa baki daya.
kalubale a siyasa
Gaskiya da farko lokacin da na shiga siyasa sai na fara dar-dar saboda yadda mutanenmu suke yi mana wani irin kallo. Saboda mutanenmu suna dauka cewa duk matar da take siyasa tamkar karuwanci take yi. Wannan ya sa a da idan aka ba ni mukami sai in nemi wata in ba ta, ni kuma in goya mata baya, daga bisani bayan na fahimci cewa kowa harkarsa yake yi ba wanda ya damu da wani, kuma yadda mutane suke dauka ba haka lamarin yake ba, sai na saki jikina na ci gaba da harkokin siyasa ba tare da wani shayi ba. kalubale na biyu shi ne su ’yan siyasa sai ka yi hakuri da su don za ka rika ganin kamar amfani suke yi da kai idan suka kai gaci su ajiye ka, amma abin ba haka yake ba, idan ka yi hakuri za ka ga ka samu nasara. Saboda haka sai ka bi a hankali sannan za ka ga hasken abin. Su ma kuma ’yan siyasar suna lura da kai har sai sun tabbatar da kokarinka sannan za su amince da kai. Wani lokaci ma za ka ga ba su son ka bar wurin da suka sanya ka saboda kokarin da kake yi.
Nasara a siyasa
Gaskiya ba komai ba ne illa jajircewa da gaskiya da kuma rikon amana. Ita siyasa ba wata aba ba ce illa bauta wa mutane, tare da cika alkawarin da ka yi musu tun lokacin yakin neman zabe. Shi dan siyasa ana so ya zama mai gaskiya da rikon amana da kuma cika alkawari. Ba kamar yadda mutane suke dauka ba cewa ita siyasa yaudara ce da rashin gaskiya da cin amana. Ni ba haka na dauki siyasa ba. Siyasa ta wuce haka, harka ce ta taimakon juna. Kuma ni ba na kyashi, duk inda na ga za a samu ci gaba nakan yi kokarin sanya wata mace a wurin, ta yadda za mu ci moriyar wurin gaba daya. Shi ma rashin kyashi da rashin bakin ciki suna daga cikin sirrin da suka sa na samu ci gaba a siyasa.
Nasarori a rayuwa
Na samu nasarori masu yawa. Tun da wadanda muke tare da su ba sa yi mana mugunta kuma ba sa yi mana kyashi, shi ya sa mu ma ba ma yi wa na kasa da mu kyashi. Kuma shi ya sa muka samu nasarori da yawa, kamar samar da ayyukan yi da koya wa mata sana’o’i iri-iri, kamar yadda ake yin sabulu da turaren kamshi da toye-toye da soye-soye da abinci da madara da yagot da man shafawa da yadda ake sarrafa kwamfuta da sauransu.
Matsalar da na fuskanta
Shi dan Adam ba ka raba shi da matsala. Babbar matsalar ita ce ta rashin fahimta daga mutanenmu, da kuma irin kallon da wasu suke yi mana na yi musu babakere. Saboda haka muke kira a gare su su ci gaba da yin hakuri da mu. Da yardar Allah duk abin da muka samu su ma za su samu.
Burina
Burina shi ne in ga iyalina cikin koshin lafiya, kuma in ga mata musamman matan Arewa da ke Legas sun samu ci gaba, a rika damawa da su ba tare da wata matsala ba. Ina ganin mata sun ci gaba.
kasashen da na taba zuwa
Na je kasar Saudiyya da birnin Dubai. Kuma na je jihohi da dama na Najeriya.
Abinci da tufafi
Na fi sha’awar tuwon masara da miyar kuka. Haka zalika na fi son kayan gargajiya namu na Hausawa. Sannan na fi son jan launi. Ka san kowa da abin da ya dame shi kuma kowa da ra’ayinsa.