Allah Ya yi wa Hajiya Bilkisu Mainasara rasuwa, a safiyar Lahadin da ta gabata da misalin karfe tara.
Marigayiyar, kafin rasuwarta, ta yi gajeruwar rashin lafiya bayan da ta gama Sallar Asuba a wannan rana.
Bilkisu, kafin rasuwarta, ma’aikaciya ce a Sashin Ilimi na Karamar Hukumar Malumfashi a Jihar Katsina. Ta rasu tana da kimanin shekara 44. Ta bar mijinta, Alhaji Tanimu Yusuf Kaka na Hukumar Ilimin Bai-Daya (SUBEB) ta Jihar Katsina da ’ya’ya biyar, maza uku mata biyu da kuma ’yan uwa da dama. Allah Ya gafarta mata da rahama, amin.