Hajiya Bilkisu mace ce da ta yi fice wajen bayar da gudunmawa wajen cigaban ilimi a Jihar Jigawa kuma ita ce ta farko a jihar da ta kafa Makarantar Standard School dake da hedkwata a garin Dutse na Jihar Jigawa. Ta kafa makarantar ce da nufin tallafa wa ’ya’yan marasa galihu da mata don su samu ilimin zamani. Hajiya Bilkisu daya ce daga cikin ’ya’yan Marigayi Alhaji Shehu Mujaddadi ce daya daga cikin manyan alkalai ne tun zamanin tsohuwar Jihar Kano. Kafin a kirkiro Jihar Jigawa mahaifin Basarake ne a cikin yankin masarautar Hadejia da ke Jihar Jigawa. Hajiya Bilkisu ta kafa makarantarta dake Dutse ce domin tallafa wa mata da marayu da ’ya’yan marasa galihu kuma ta yi karance karance masu yawa. Ta rike mukamai daban daban a tsakanin gwamnati da bankuna da kungiyoyi da ba na gwmnati ba. Hajiya Bilkisu mace ce mai tausayi musamman wajen tausaya wa almajirai da marasa galihu.
Wakilimmu Umar Akilu Majeri ya samu ikon zantawa da ita kuma ga yadda hirar ta kasance:
Tarihin rayuwata
Dafarko dai sunana Bilkisu Goggo Shehu Mujaddadi Hadeja, Daraktar Makarantar Standard da ke Dutse. An haife ni a garin Hadeja a shekarar 1966. Mahaifina Mujaddadi Alkali Shehu. Na yi karatun firamare a makarantar firamaren da ke Unguwar Dallaa garin Hadeja wadda a halin yanzu ake kira da Abdulkadir Primary School a Hadeja. Daga nan na wuce sakandaren Shekara da ke Jihar Kano a lokacin Jigawa tana karkashin Jihar Kano. A 1978 na cigaba da karatun sakandare a makarantar Santilus da ke Bomfai duk a cikin garin Kano. Bayan na kammala sakandare sai na wuce makarantar Share Fagen Shiga Jami’a (CAS) na yi karatun share fagen shiga jami a daga nan na samu shiga sami jami ar Bayero da ke Kano a shekarar 1990. Bayan na kammala digirina na farko sai natafi bautar kasa kasancewar na yi digirina a fannin turanci sai na fara yin aiki da Bankin Union (Union Bank) inda nayi shekaru hudu. Daga baya na sake komawa makaranta na yi shekara daya sai na sake yin aiki da NIC a Abuja. Daga nan ne na kama aiki da Bankin Sterling amma a lokacin yana Marchant Bank a shekarar 2002.
Na rike mukamin mai bai wa Gwamna Shawara a fannin tara kudi da sayar da hannun jari a lokacin Gwamnatin Ibrahim Saminu Turaki a shekarar 2004. Na sake zama mai ba shi shawara a bangaren harkokin kasuwanci da masana’antun gwamnati na Jahar Jigawa. Daga nan bayan Samiinu ya bar gwamnati sai na yi aiki da wasu kungiyoyi da ba na gwamnati ba ciki har da wata kungiya da ake kira DDI wadda take karkashin kulawar United Debelopment Foundation (UDF). A shekarar 2008 na sake komawa Jami ar Bayero na cigaba da karatun digiri na biyu watau Masters. Daga nan na yi tafiye- tafiye zuwa kasashen duniya inda kewaya duniya gwargwadan hali. Na yi yawo ne domin na samu ilimin yadda zan tafiyar da harkokin makarantata kafin in kafa ita wannan makaranta da nake ciki a halin yanzu. Bayan na dawo ne a 2010 na samu wuri na kafa wannan makarantar aka fara karatu.
Me ya ba ki sha’awar kafa wannan makaranta?
Kishin jihata da al ummata da tunanin in taimakawa ’yan uwana ya sa na kafa wannan makarantar. Don a wancan lokaci lokacin da muke cikin gwamnati ina jin magangagun marasa dadi a duk lokacin da muka yi tafiya da Kwamishiniyar ilimi ta wancan lokacin a zamanin gwamnatin Saminu Turaki ana yi mana gori ana cewa jihar mu babu wurin kwana, babu makarantu, babu motocin hawa. Jiharmu kauye ce, sai na ga babu wanda zai raya mana jiharmu dole sai mun raya ta da kanmu. Wannan ya sa na yi tunanin kafa makarantar domin a daina yi mana gori, ana cewa jihar mu babu makarantun kudi. Da yake a wancan lokacin babu asibiti mai inganci kamar yanzu, babu isassun gidajen ma aikata ban yi ba sai a wannan gwamnatin da ta gabata ta Gwamna Sule Lamido, domin ba zai yiwu ka dauko malami ba shi da wurin kwana, ba asibitin da zai kai iyalansa in ba su lafiya da sauransu ka ajiye shi, hakan ta sa sai a wannan lokaci na kafa makarantar.
Me ya sa mata suka zama koma baya a fagen ilimin zamani?
Na farko dai akwai rashin wadata daga wajen iyaye mata, domin karatun mata a kauye ko a karkara mata iyayensu ne ke daukar nauyin karatunsu. Kusan iyaye maza suna nuna halin ko in kula a kan yadda rayuwar ‘ya’ya mata ke tafiya. Hakan yana da nasaba ne da al’ada irin ta Malam Bahaushe, kuma hakan yana da nasaba da karancin samu a wajan iyaye mata domin wasu matan sai sun yi aikatau suke iya ciyar da kansu. Su kansu magidanta a yankunan karkara ba kowane yake iya daukar nauyin ciyar da iyalansa ba ballantana a ce ya yi masu sutura, ballantana kuma a ce ya saka yaran a makaranta. Za ka ga yara masu hazaka da kwazo amma babu mai daukar nauyin karatunsu saboda iyayensu ba su da galihu.
Ba komai ba ne y asa ‘ya’ya mata ba sa yin karatun zamani duk da wayewar kan da muke da shi a halin yanzu da ya wuce rashin kudi. Mutane a yankunan karkara suna fama da talauci sannan a bangaren al’ada a nan arewa ba a bai wa ‘ya’ya mata mahimmanci a fagen karatun zamani musamman iyayensu maza sun fi karka ta a bangaran karatun ‘ya’yansu maza saboda su abinda suka dauka shi ne karatu na da namiji ne, mace kuma in ta kai munzalin aure a yi mata.
Mene ne burinki a rayuwa?
Babban burina a rayuwa shine na ga ‘ya’ya mata sun samu ilimin zamani, suna fafata wa da maza a fagen neman karatun zamani domin ina son na ana damawa da mata a ayyukan gwamnati.
Me ya fi bata miki rai?
A gaskiya ba na son na ga ana zagin almajirai musamman idan na ga na ci musu mutunci idan suka yi danfami a kan tituna suna bara sai na ji ba dadi. Idan na ga ana zaginsu ba na jin dadi. Idan na ga ana wulakantasu ba na jin dadi. Da a ce gwamnati za ta yarda sai ta kafa makaranta wacce za ta rika baiwa almajirai ilimin zamani, musamman almajiran makarantar toka wadda suke almajiranci domin yin hakan zai taimaka wajen wayar wa almajiran kai a fannin rayuwa ta yau da kullum
Da yake na ga kina son almajirai kuma ga shi kina da makaranta ta boko, wace irin gudunmawa kike baiwa almajiran?
Sau da yawa ina son in ba da gudunmawa ga almajiran wajen ba su guraban karatu a amakarantata amma saboda ban samu hanyar da za ta hada ni da su kai tsayeba shi ya sa ban yi ba. Ka san ba zai yiwu ba a ce ka je ka dauko yaro yana gaban malaminsa ka ce za ka sanya shi a boko ba alhalin su iyayensa karatun allo suka tura shi.
Hajiya Bilkisu Goggo: Baya mai goya marayu
Ba kowane zai amince da hakan ba. Amma ko yanzu idan akwai almajirin da yake da sha’awar karatun boko in ya zo makarantata zan ba shi gurbin karatu a duk shekara. Zan bayar da guraben karatu guda biyar domin almajirai masu nazarin Alkur’ani su samu ikon karatun zamani daga matakin nursery zuwa na firamare aji shida kyauta har yaro ya kammala.
Ni burina shi ne in tallafa wa almajirai, yanzu haka ina shirin tallafa wa marayu wadanda mahaifansu suka mutu su kuma suna karatu a makarantata daga ranar da aka ce babu ran mahaifinsu daga ranar ni kuma na daukewa ‘ya’yansa duk kudin da suke biya na makaranta komai yawansu har su kammala karatunsu. A duk shekara na kan dauki yara uku in ba su gurbin karatu kyauta, amma fa wannan damar ta yara masu rangwamen gata ce kawai. Ina amfanida mai unguwa ne domin zakulo ‘ya’yan marasa gata a unguwanni in taimaka masu.
Kuma kamar a nan Unguwar Yalwawa inda makarantar take saboda wadanda suke unguwar su ma suci moriyar shirin karatun, na baiwa mai unguwa damar bayar da sunayen ‘ya’yan marasa karfi gurbin karatu uku a duk shekara.
Hanyoyin da za a bi a gyara ilimi
Hanyoyin da za a bi wajen gyara ilimi ba wasu masu wahala ba ne domin yadda aka bi aka lalata haka za a bi agyra, duk da cewa gyaran ya fi wahala. Domin ai da ma mu ne muka lalata kuma mu da muka lalata mun san hanyar da za mu bi wajen dawo da martabar ilimi a kasar nan.
In za a yi adalci kamata ya yi dalibai masu daukar darasi kada su wuce mutane 30 a aji sabanin haka za ka ga dalibai kamar 150 a aji daya musamman a makarantun gwamnati to in za a yi adalci ta yaya yaro zai iya karatu a irin wannan yanayi ballantana ya sami fahintar abin da malami yake koya masa. Shi ma malamin zai zama ba shi damar iya duba dalibai a cikin minti 40 da aka ware masa domin koyar da dalibai saboda yawan daliban ya wuce ka’ida a cikin aji yayin da su kansu masu makarantun kudi suke bude makaranta su kuma su tafi kasuwanci wata jahar ko Abuja suna neman kudi ba sa tsaya wa su sa ido akan yadda harkokin koyarwa yake tafiya a makarantun sakamakon haka ya sa ba a samun koyarwa a makarantun yayin da awasu makarantun ba a iya daukar kwarrarrun malamai da za su iya koyar da dalibai kamar yadda ya kamata.
Na ga malaman firamare a wasu sassa na jihar da ba su kammala sakandare ba amma saboda gata an dauke su suna koyarwa a makarantun firamare. Wallahi ko ABCD ba za su iya rubutawa ba amma wai malamai ne, ta yaya malamain da bai iya karatu da rubutu ba zai koyawa wani har ya fahimci abin da ake so ya sani? Saboda haka gyaran ba na gwamnati ba ne kadai ba dole sai mun hada hannu wuri guda mun yi wa kasa aiki sannan ilimi zai gyaru.
Yawon duniya
Na yi yawo kasashen duniya amma domin neman yadda zan kafa makarantata kuma in gano hanyoyin da zan tallafa wa harkokin ilimi a kasata da jihata. Babu kasar da ta burge ni a fagen ilimi kamar Ingila. Domin a Ingila ba za ka iya bambance tsakanin makarantun kudi ba da na gwamnati ba saboda suna da tsari wajen tafiyar da makarantunsu. Ingila ta burge ni fiyeda kowacce kasa daga cikin kasashen da na ziyarta.