Hajiya Amina Yuguda haifaffiyar Yola ce da ke jihar Adamawa. Takasance mai yada labarai a gidan talabijin da ke Yola a jihar Adamawa. Ta kasance mai sha’awar harkar yada labarai tun tana karama.
Tarihina
Sunana Amina Ibrahim Yuguda ni ‘yar Yola ce da ke jihar Adamawa,amma a jihar Legas na girma. Mahaifina shi ne Ibrahim Yuguda dan kasuwa ne wajen tafiyar da harkar jiragen sama .Mahaifiyata kuma ta kasance ma’aikaciyar banki.Mu shida ne a wajen mahaifiyarmu,biyar mata namiji daya.
Na yi karatun digiri a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria inda na karanci yadda ake labarai da na gama sai na yi digiri na biyu a fannain sadarwa a jami’ar Modibbo Adama da ke Yola a jihar Adamawa. Ni kuma yar yada labarai a Telebijin din Gotel dake Yola a jahar Adamawa. Na kasance mai son yada labarai da kuma abin da ya kunshi ado da kwalliya.
Na fara aiki a shekara 2006 a FRCN Kaduna. A shekara ta 2010 na koma harkar ’yan yada labarai na Kaduna daga nan na yi aiki da hukumar tallace-tallace ta manema labarai (Media Staff adbertising agency) da ke Legas. Daga nan na samu aiki a gidan talabijin da ke Gotel a shekara 2012 zuwa yanzu.
Wanda na fi shakuwa a iyayena
A gaskiya ni ’yar lelen mahaifina ce, mun shaku da shi sosai. Tun lokacin da nake karama, mahaifina bai kasance mai tsananta mana ba. Mahaifiyata ta kasance mai kula da tabbatar da tarbiyarmu don haka tana da zafi.
Irin halayyar da na gada daga iyayena
Mahaifina ya kasance mutum ne mai gaskiya da fadin gaskiya. Kuma idan har ya ce zai yi abu to inAllah ya yarda sai ya yi. Haka kuma idan ya ce ba zai yi abu ba, ba ya yi. Ina ganin wadannan halayen nasa zan iya cewa na gada.
Idan fadin gaskiya zai sa ni na bata wa mutum rai, na gwammaci na fada wa mutumin gaskiya a maimakon na yi karya ko kuma yaudara.
Mahaifiyata ta kasance mai kamun kai da natsuwa. Zan iya cewa na gaji wannan.
Burina ina karama
Ina son wasanni da kuma sha’awar ganin masu yada labarai a gidan talabijin da na rediyo. Nakan kwaikwaye su ,kuma ina da burin cewa wata rana zan kasance mai yada labarai ko a gidan talabijin ko kuma na radiyo.
Abin da ba zan manta da shi ba ina karama
Abu na farko shi ne girman Legas da kuma yadda mahaifina yake ba mu lokacinsa a kowace Asabar. Mukan je ganin tekun Legas da yayyena da kannena, mu yi wasa kuma a samu lokacin nishadi da juna. Ba zan taba mantawa da wannan ba.
Abin ado da yake burge ni
Ina son gilashi sosai kuma ina son sanya suturar da ba za ta matse ni ba. Ina son sanya kaya sakakku wandanda ba za su takura ni ba. Kuma don ana yayin abu a kasuwa ba shi zai sanya ni sha’awar sayan kayan ba. Nakan sanya suturar da nake ganin ta yi min kyau ba don ana yayinta ba. Kuma ina son atamfa sosai.
Shakatawa
Na fi son zuwa shakatawa a duk inda ruwa yake .Ina son zuwa Abuja hutu domin ba abin da ba za ka samu ba idan kana Abuja. Amma in dai waje ne na fi son zuwa inda ruwa yake.
Wandanda suke burge ni
Mahaifana su ne suke burge ni.Mahaifina tun ina karama yakan ba ni shawara a kan abubuwa da dama kuma yana yawan bani shawara a kan kamun kai a matsayina na Musulma. Mahaifiyata kuma saboda yadda ta kula da mu ga shi tana aiki kuma tana kula da mu har ya zuwa yanzu.
Turaren da nafi so
Ina son turaren Elizabeth Arden da kuma su humrah da sauransu.
Macen da take burge ni
Kada a ce don sun yi nasarar zabe. Amma Hajiya Aishatu Buhari matar Shugaban kasa tana burge ni. Domin ita ce macen da ta mara masa baya da kuma ba shi goyon baya a duk lokuta da shekarun da suka yi na kamfe domin cimma burinsu. Don haka na jinjina mata kwarai.
Mutane da dama sun manta cewa cin zaben nan ya faru ne da taimakon Allah da kuma na matar Janar Buhari domin ita ce matar da take kwantar masa da hankali da kuma ba shi hakuri a koda yaushe. Idan na ganta a yau zan ce mata “Barka da samun nasara” kuma barkanta da goya wa Baba Buhari baya.
Shawara ga masu karatun jarida a jami’a
Kada su manta cewa dagewa da karatu da koyon aikin shi ne mafi mahimmanci. Sannan kuma su sanya a zukatunsu cewa Musulmai da Kirista duk daya ne kuma idan an fara aikin ana fadin gaskiya.
kalubale da na fuskanta
Babban kalubalen shi ne idan har mace ta kasance yar Arewa ce aka gan ta tana aiki sai a yawaita tsawata mata cewa lallai sai ta fito da miji. Akan manta cewa komai da lokacinsa. Amma ni kam yanzu aikina shi ne mafi mahimmanci a gare ni domin iyayena suna yi min duk abin da nake so.
kalubale na biyu shi ne aiki da maza. A gaskiya da wahala amma sai an dage domin akwai maza da ba su son mace ta saka su aiki. Gani suke yi kamar a ce kaskanci ne mace ta saka su aiki nan. Idan matsayinka ya fi na su kuma ana son komai ya tafi dai-dai dole ne a saka su aiki. Babban kalubalen da nake fuskanta shi ne yadda zan musu magana a cikin lumana yadda ba za su ji an kaskantar da su ba a kullum.
Abin da nake so a tuna ni da shi
Ina son a tunani a matsayin macen da ta rike kanta ko cikin jin dadi ko rashinsa domin cimma burina na yada labarai a gidan talabijin.