✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hafsan soja ‘ya kashe kansa’ a Kaduna

Ana zargin ya kashe kansa gabanin kotun soji ta yanke mishi hukunci

Ana zargin wani hafsan soja mai mukamin Manjo ya kashe kansa a Jihar Kaduna.

Manjo UJ Undianyede, wanda tsohon kwamanda ne da ya jagoranci yaki da Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas, ana zargin ya kashe kansa ne kafin wata kotun soji da aka gurfanar da shi a gabanta ta yanke mishi hukunci.

Majiyoyinmu na soji sun shaida mana cewa Manjo UJ Undianyede ne ya harbe kansa ne kimanin sa’a 72 kafin kotun sojin ta yanke mishi hukunci kan zargin aikata wasu laiufuka a lokacin da yake kwamandan yaki da ta’addanci.

Majiyoyin sun ce ya harbe kansa ne ta hanyar amfani da karamar bindigarsa a harabar jami’ar sojoji ta NDA da ke Kaduna a ranar Litinin.

“Ina ganin ya kashe kansa ne saboda hukuncin da kotun soja za ta yanke gobe (Alhamis 19 watan Mayu, 2022). Sai yau (Laraba) muka samu labarin rasuwarsa.

“A lokacin da yake jagorantar yakin, ana zargin shi da wasu abokan aikinsa da aikata wasu laiufuda da a kansu aka gurfanar da su a Babbar Rundunar Soji ta 1 da ke Kaduna,” inji daya daga cikin majiyoyinmu na soji ranar Laraba da dare.

Aminiya ta samu rahoto cewa ana zargin mamacin ne da aikata almundahana da watsi da aiki, tsaurin ido, sakaci da aiki da dai sauransu.

Wata majiyar kuma ta alakanta rasuwar da tsananin damuwar da Manjon yake ciki, saboda ya dade a fagen yaki da Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas.

Manjo Manjo UJ Undianyede yana daga cikin rukuni na 55 da aka yaye daga NDA, kuma a watan Satumba ake sa ran yi musu karin girma zuwa mukamin Laftanar-Kanar.

Mun tuntubi kakakin Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu, kan lamarin amma ya ce bai samu labari ba.

Amma da muka tuntubi mai magana da yawon NDA, Manjo Bashir Jajira, ya karyata labarin, yana mai cewa babu wani hafsan soji da ya kashe kansa.

“Babu wani jami’in NDA ya da kashe kansa kamar yadda ake yadawa, a halin yanzu mu dalibanmu kananan hafsoshi suna Kachia inda suke atisayen harbi, ba sa cikin makarantar. Babu wani abu makamancin haka da ya faru,” inji Manjo Jajira.

Shi kuma Mataimakin Daraktan Yada Labarai na Rundunar Soji ta 1da ke Kaduna, Manjo Musa Yahaya da muka tuntube shi, ya ce ba shi da masaniyar wata kotun soji da ke zama a rundunar.

Daga Sagir Kano Saleh, Idowu Isamotu (Abuja) & Maryam Ahmadu-Suka (Kaduna)