✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hadarin mota ya kashe mutum daya da shanu 4 a Kaduna

Wani mutum guda da kuma shanu hudu sun rasa rayukansu a wani mummunar hadarin mota da ya auku a gab da shataletalen Lugard Hall a…

Wani mutum guda da kuma shanu hudu sun rasa rayukansu a wani mummunar hadarin mota da ya auku a gab da shataletalen Lugard Hall a tsakiyar garin Kaduna.

‎Hadarin ya auku ne da misalin karfe 12 na daren ranar Talata a lokacin da wani direban tirila mai dauke da shanun ta fadi a lokacin da yake kokarin wuce shataletalen.

Aminiya ta samu bayanin cewa, mutum daya ne ya rasu a asibiti sannan mutum biyu kuma an kaisu asibiti a sakamakon rauni da suka samu.

‎Wakilinmu ya ruwaito cewa, har zuwa safiyar Laraba mattatun shanun na watse a gefen titi inda su kuma sauran da ke a raye ke a gefe guda.

A cewar wani da ke kusa da wurin da abin ya faru ya shaidawa Aminiya cewa, direban ya samu hadarin sakamakon shi bako a hanyar garin, hakan yasa bai da masaniyar akwai shataletalen. ‎

Mataimakin Kwamanda na hukumar kiyaye hadurra Salisu Umar Galadanci, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce, an kwashe marasa lafiyan zuwa asibitin Barau Dikko.

Ya kuma shawarci direbobi da su kaucewa tukin dare ba tare da suna da kwararrun mataimaka ba.