Rahotanni sun bayyana cewa wani mummunan hadarin kwale-kwale ya yi sanadin mutuwar mutane 15 a Karamar Hukumar Shagari da ke Jihar Sakkwato.
Shugaban Karamar Hukumar Shagarin, Aliyu Dantanin Shagari, wanda ya tabbatar da hakan ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Talata da maraice.
Muryar Amurka ta ruwaito Dantanin yana cewa, mutum 25 ne a cikin kwale-kwalen da ke kan hanyar zuwa wurin Mauludi a lokacin da hadarin ya faru.
Yankin Shagari ya sha fuskantar wannan matsala ta hadarin kwale-kwale wadda kuma ke zama dalilin mutuwar mutane da dama.
Aukuwar wannan matsala ce ta sanya a wata ziyarar ta’aziyya da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya kai, ya yi wa al’ummar yankin alkawalin samar da riguna masu taimakawa wajen hana nutsewa cikin ruwa idan aka samu irin wannan matsala.
Masharhanta sun sha yin tsokaci akan hadurran kwale-kwale da yadda ya kamata mahukunta da jama’a su sa ido don kaucewa aukuwar matsalar.
Farfesa Bello Badah, mai sharhi akan lamurran yau da kullum, na ganin amfani da tsofaffin kwale-kwale na daga cikin abubuwan da ke haddasa hadarin da kuma yadda ake daukar mutane da kaya fiye da kima.
Ya kuma ce ya kamata mahukunta su sa ido don tabbatar da ana amfani da kwale-kwalen da ya dace da kuma adadin jama’a da kayan da suka dace.
Baya ga ayyukan ’yan ta’adda da kuma hadarin mota a wasu sassan Najeriya, matsalar hadarin kwale-kwale na daga cikin matsalolin da ke lakume rayukan jama’a.