Fitaccen malamin Musulunci a Kano, Sheik Muhammad Bin Uthman ya ce kasuwancin kudaden intanet na cryptocurrency haramun ne a Musulunci.
Sheik Bin Uthman ya kuma shawarci jama’a da su guji harkar saboda illar da ke tattare da ita, kasancewar yawancinsu na shiga harkar ne da ganganci ko kuma a jahilce.
Shehin malamin wanda kuma shi ne Babban Limanin Masallacin Juma’a na Sahaba da ke unguwar Kundila a Kano, ya ba da fatawar ne yayin wani karatu da ya gabatar mai taken ‘Hakkokin Musulmi Guda Shida’ a ranar Lahadi.
A cewar malamin, “Shi kansa wanda ya kirkiro kudin [Satoshi Narcomoto] yana musanta cewa shi ne ya kirkiro tsarin, to ka ga ta fuskar asali ma ana kai-kawo kan wanda ya kirkiro shi.”
A kan haka ne ya ja hankalin Musulmai da su kaurace wa shiga tsarin, duba da irin hatsarin da ke tattare da shi.
“A farkon fitowarsa, duk Bitcoin yana daidai da Senti daya na Amurka, yanzu kuma kowanne daya sai ka ba da Dalar Amurka 11,000 za a ba ka. Ka ga abin ai ya zama hauka.
“Kuma wannan kudi idan ka ce za ka yi harka da su, idan suka karye ba wanda za ka kama ka ce ya biya ka, tunda babu wata kasa da ta yarda da shi don haka ba kudi ba ne,” inji shi.