Gwamnatin Habasha ta dauki matakin dakatar da bai wa ’yan Najeriya biza bayan sun isa kasar.
Masu ruwa-da-tsaki na ganin cewa, matakin wanda ya fara aiki nan take, zai haifar da cikas ga sha’anin tafiye-tafiye zuwa kasar.
- NUT ta bukaci gwamnoni su biya malamai basussukan da suke bi
- Kotu ta raba auren shekara 1 saboda rashin soyayya
Tuni dai hukumar sufurin jiragen sama ta kasar ta sanar da abokan huldarta sabon matakin da aka dauka.
Cikin sanarwar da ya aike wa abokan kwasuwancinsa kamfanin Ethiopian Airlines ya ce, “ku sani daga yanzu an dakatar da bayar da biza ga ’yan Najeriya a kasar Habasha.”
Kamfanin Jiragen Kasar Habasa (Ethiopian Airlines) na daya daga cikin mashahuran jiragen sama na ketare da ke zirga-zirga a Najeriya.
Kafin wannan lokaci, fasinjojin da suka tafi Habasha daga Najeriya za su iya samun biza cikin sauki da zarar sun isa Babban Filin Jirgin Sama na Bole da ke Addis-Ababa, babban birnin kasar.
Amma da wannan sabuwar dokar, dole ne ga masu bukatar zuwa kasar daga Najeriya su mallaki bisar ET a ofishin jakadancin kasar da ke Abuja.