✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Habasha da Eritrea sun kaddamar da gagarumin hari kan ’yan tawayen Tigray

Kungiyar TPLF ta ce kasashen biyu sun kaddamar da gagarimin harin ne a ranar Alhamis.

Kasar Habasha da Erirea sun kaddamar da wani gagarumin harin hadin gwiwa kan kungiyar yakin kwatar yancin Tigray (TPLF).

Kungiyar TPLF ta ce kasashen biyu sun kaddamar da gagarimin harin ne a ranar Alhamis, bayan sun tura sojoji da kayan aiki masu yawa zuwa kasar Eritrea, a shirinsu na mamaye yankin Tigray.

Wani kakakin TPLF, Getachew Reda, a shafinsa na Tuwita na cewa, “Mayakan kungiyar na kare inda suke,” duk da cewa ana musu “ruwan bama-bamai “ a wasu wuraren da suke rike da su.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya gaza tabbatar da wannan ikirari, kasancewar shiga yankin Arewacin Habasha ba zai yiwu ba, sakamakon hatse layin sadarwar intanet da sauran hanyoyin sadarwa sama da shekara guda.

An ci gaba da fada ne a tsakanin gwamnati da ’yan tawayen TPLF a makon da ya wuce bayan wani tsaiko na watanni biyar da aka samu.

An soma fadace-fadacen ne da kai hare-hare ta jiragen sama da kuma ta kasa ga yankin Tigray, wanda hakan ya rusa fata da ake da shi warware rikicicin cikin ruwan sanyi a yakin da bangarorin ke yi sama da shekara biyu.