✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnonin da suka koma Jam`iyyar APC, na batun kaiwa ga nasara

Bayan wani taron awa hudu da Gwamnoninnan bakwai da ake wa lakabi da Gwamnonin sabuwar PDP suka yi da shugabannin jam`iyyar APC, a masaukin Gwamnan…

Bayan wani taron awa hudu da Gwamnoninnan bakwai da ake wa lakabi da Gwamnonin sabuwar PDP suka yi da shugabannin jam`iyyar APC, a masaukin Gwamnan Jihar Kano da ke Abuja a ranar Talatar makon jiya, an jiyo shugaban jam`iyyar sabuwar PDP Alhaji Abubakar Kawu Baraje yana shaida wa taron manema labarai sanarwar bayan taron da suka cimmawa tsakanin su da jam`iyyar APC, wadda ta tabbatar da cewa daga ranar sun hade da jam`iyyar APC, sun sarayar da tsagin su na sabuwar PDP. (Kodayake masana shari`a sun tabbatar da cewa sabuwar PDP din ba jam`iyya ba ce, don bata da rijistar kanta).
Wannan sanarwar hadewa da ta samu halartar akasarin shugabannin jam`iyyar APC a karkashin jagorancin shugabanta na riko Cif Bisi Akande, ya yin da daga bangaren sabuwar PDP, akwai shugaban jam`iyyar Alhaji Kawu Baraje da tsohon Gwamnan Jihar Kwara, Sanata Bokola Abubakar Saraki da Gwamnonin jihohin Kwara da Kano da Adamawa da Ribas dana Neja, Dokta Mu`azu Babangida Aliyu, wanda ana daf da kammala taron ya fice daga wurn taron, daga bisani kuma bayan ya ji takwarorin nasu sun bayar da sanarwar sun fice daga sabuwar PDP sun hade da jam`iyyar APC, ya sa Sakatarensa na yada labarai Danladi Ndayebo, ya bada shelar cewa bada shi ba, shi yana nan zama daran-dam cikin jam`iyyar PDP.
Shi ma Alhaji Sule Lamido na jihar Jigawa, wanda ko wajen taron na Abuja bai je ba, bayan jin shelar hadewar, ya sa Sakatarensa na yada labarai Alhaji Umar Kyari, ya bada sanarwar cewa shi ma yana nan cikin PDP bai fiita ba kuma baya da niyyar fita, duk kuwa da mawuyacin halin da yake ciki na Hukumar yaki da ta`annati da haramtattun kudade, wato EFCC, ta kama `ya`yansa biyu tana zarginsu da hada-hada da kudaden haram, zargin da ya ce tuni wasu suka gasgata shi.
A gefe daya an ruwaito Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko, yana shaidawa manema labarai cewa duk da ba a ga keyarsa ba a wajen wancan taro, bisa ga dalilin baya kasar nan a wancan lokacin, amma ya tabbatar da cewa yana cikin waccan tafiya ta komawar takwarorinsa hudu cikin jam`iyyar APC. Shi kuwa gwamnan Jihar Adamawa Alhaji Murtala Nyako, ruwaitosa akai yana  bada tabbacin cewa gwamna Sule Lamido na jihar Jigawa da takwaransa na Jihar Neja Dokta Mu`azu Babangida Aliyu, su ma suna nan tafe a cikin  tafiyar jam`iyyar APC a watan Janairun sabuwar shekara in Allah Ya kaimu.
Idan mai karatu bai manta ba, kafin gwamnoninnan su kai gazama bakwai, sun fara ne da gwamnoni uku rak, wato gwamnonin Jihohin Jigawa da Sakkwato da Adamawa, wadanda suka rinka tarurruka da kai ziyara ya  junansu, basu zama bakwai ba, sai a `yan watannin baya da jam`iyyar PDP ta yi babban taronta na musamman na kasa baki daya, inda su kuma wadancan gwamnoni bakwai suka fice daga dakin taron a karkashin jagorancin tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, inda suka je Cibiyar taro ta Shehu Musa `Yar`aduwa, suka zabi nasu shugabannin a karkashin jagorancin Alhaji Kawu Baraje.
Tun daga wancan lokaci aka shiga ja-in-ja tsakanin gwamnonin bakwai da uwar jam`iyyar ta PDP. Bukatun da gwamnonin suka gabatar sun hada da lalle sai a janye dakatarwar da aka yi wa gwamnan jihar Ribas Mista Rotimi Amaechi, sannan kuma a amince da cewa shine halastaccen zababben shgaban kungiyar gwamnonin kasar nan, a kumasauke shugaban jam`iyyar na kasa baki daya Alhaji Bamanga Tukur, a kuma mayar da shugabancin jam`iyyar ta PDP a jihar Adamawa, wanda yake bangaren gwamna Nyako, dama dai tuni suka janye neman da suka yiwa shugaban kasa Dolta Goodluck Jonathan na kar ya tsaya zaben 2015.
Kafin duk wadannan gwamnoni sukai matsayin ficewar da suka yi yanzu, sai da suka dauki lokaci suka ziyarci dukkan tsofaffin shugabannin kasar nan na soja da farar hula, inda daya-bayan-daya suka rika shaida masu halin rashin fahimtar da ke tsakaninsu da uwar jam`iyyarsu ta kasa, wala alla ko su sa baki a gyara. Irin yadda gwamnonin suka rinka kai waccan ziyara ga tsafaffin shugabannin kasa, haka suma ayarin jiga-jigan jam`iyyar APC suka rinka kai masu zawarcin su shigo cikin APC.
A yanzu maganar da ake, shigar gwamnonin biyar ta sake canja tsarin zaman jam`iyyu siyasar kasar nan. Alal misali, yanzu gwamnonin PDP sun koma 18, maimakon 23, ya yin dana APC suka tashi daga 11, zuwa 16. Jam`iyyun APGA da LP kowace na da jiha daya, wato Anambra da Ondo Haka a Majalisun Dokoki na kasa, idan har `yan Majalisun Dokokin wadannan jihohi sun bi gwamnoninsu, to, PDP mai Wakilai 208a Majalisar Wakilai ta tarayya zata koma da 168, ya yin da APC mai Wakilai 138, za ta koma mai Wakilai 178. Samuwar hakanzai sanya mikamai irin nasu mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai da shugaban gidan da mataimakinsa da Bulaliyar Majalisar da mataimakinsa, duk za su kubuce wa jam`iyyar PDP, su koma hannun APC.
   Tabbatuwar wannan hadewa ba karamar guguwar canji baceda take kadawa a cikin siysar kasar nan dangane da karatowar zabubbukan shekarar 2015, da mutanen kasa suke begen samun canji, amma haka ba zai tabbata ba har sai idan shugabannin daza a dama dasu cikin tafiyar ta APC, sun taru sun hada kai, wajen gudanar da kome cikin gaskiya da adalci, wajen tabbatar da barin demokradiyyar cikin gida ta yi aiki akan zabenshugabannin jam`iyya tun daga tushe zuwa na `yan takarar da mutane suke so ba nadi ba kamar yadda shugabannin siyasar kasar nan suka saba yi.
Ba wani abu ya sa nike batun tabbatar da yin gaskiya da adalci a wannan tafiya ba, sai don sanin da na yi tun tafiya bata yi nisa ba a jihohi irinsu Kano da Sakkwato da Adamawa an fara samuntakun sakar wa ke shugaba,s  gwamna mai ci ko shugabannin da suka haifi APC suka kuma yanke mata cibi? Sannan kuma a irin wannan lokacin ne za a yi ta takatsantsan da masu fuska biyu suna cikin sabuwar tafiya suna kuma kai rahoto ga gwamnatin tarayya da aniyar su karya tafiyar baki daya. Allah dai Ya raba Yari da barawo a wannan tafiya