✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnoni na amfani da ɓata-gari wajen maguɗin zaɓe —Jonathan

Idan ka je wasu jihohi, gwamnoni sun shagaltu da ƙarfafawa masu laifi saboda siyasa.

Tsohon shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan ya yi zargin cewa wasu gwamnonin jihohi sun shagaltu da ƙarfafawa masu aikata laifuka don amfani da su wajen cimma manufar siyasa, maimakon ƙarfafa gwiwarsu su zama ƙwararru a ma’aikatun gwamnati.

Jonathan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Benin yayin da yake ƙaddamar da sakatarorin jihar da Gwamna Godwin Obaseki ya gyara.

Tsohon shugaban ƙasar ya ce, lokacin da shugaban ma’aikatan ya bayyana cewa Obaseki ya ɗauki waɗanda suka kammala digiri na farko aiki, ya ji daɗi matuƙa, yana mai cewa “yana buƙatar wani mai hangen nesa kamar Obaseki ya yi hakan”.

Ya ce, “A gaskiya idan ka je wasu jihohi, gwamnoni sun shagaltu da ƙarfafawa masu laifi saboda siyasa, waɗanda za su yi musu maguɗin zaɓe, ɗauke akwatunan zaɓe riƙe da wuƙaƙe suna bin mutane a lokacin zaɓe.

“Amma ɗaukar aikin kana ƙarfafa masu ƙwaƙwalwa a jihar Edo. ƙwaƙwalwar ba ta fito daga jam’iyyar siyasa ɗaya ba, ta fito ne daga dukkan jam’iyyun siyasa. Ƙwaƙwalwar ta fito ne daga dukkan waɗanda ke goyon bayan duk ɗan takarar gwamna.

“Waɗanda suke yin digiri na farko su yi gwagwarmayar shiga samun sakamako na matakin farko maimakon shiga ƙungiyoyin asiri da shan barasa da yi wa mata fyaɗe. Ya kamata ku yi ƙoƙari ku sami maki mai kyau. Don haka, idan kuna da damar zuwa makaranta, ku ɗauki makarantarku da mahimmanci.

Jonathan ya lura cewa, Obaseki baya goyon bayan wasu domin yana son ya ci zaɓe, sai dai don yana son gina jihar ne, inda ya ƙara da cewa: “ Ku gina jiha sai ku gina mutane”.