✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnoni ke daukar nauyin bangar siyasa —Alkali Baba

Tashe-tashen hankula na siyasa ta kowace hanya, laifi ne a karkashin Dokar Zabe.

Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya dora alhakin karuwar tashe-tashen hankula sanadiyar siyasa a kasar kan wasu gwamnonin jihohi.

Baba ya bayyana haka ne a wata ganawa da ya yi da shugabannin jam’iyyun siyasa da sauran masu ruwa da tsaki a ranar Alhamis a Abuja.

Ya ce an kira taron ne domin jan hankalin shugabannin jam’iyyun siyasa kan yadda ake samun karuwar tashe-tashen hankula a siyasance da kuma gaba a tsakanin magoya baya.

“Muna ta samun rahotannin wasu Gwamnonin Jihohi da ke karfafa wa ‘yan barandan siyasa.

“Suna amfani da kayan tsaro na kananan hukumomin da ke karkashinsu domin dakile ayyukan yakin neman zabe na jam’iyyu ko ‘yan takarar da suke da sabanin ra’ayin siyasa.

“Suna amfani da damarmakinsu wajen hana wasu yin talla a allunan talla.

“Suna kuma hana ‘yan adawar siyasa gudanar da yakin neman zabensu ko na siyasa cikin lumana wanda ya saba wa Dokar Zabe,” in ji shi.

Ya kuma dora alhakin mafi yawan tashe-tashen hankula a kan tsattsauran ra’ayi na siyasa, rashin fahimta, rashin hakuri, kuskuren siyasa, kalaman kiyayya da na tunzura jama’a.

Ya ce tashe-tashen hankula na siyasa ta kowace hanya, laifi ne a karkashin Dokar Zabe kuma laifi ne a karkashin manyan dokokin laifuka na kasar nan.

Alkali Baba ya ce ‘yan sandan Najeriya da sauran hukumomin tsaro za su cika alkawarinsu na yin aiki tukuru don tabbatar da zaman lafiya a harkokin siyasa da tsaron kasa.

Ya yi alkawarin daukar matakan da suka dace don ganowa tare da kama duk wani dan siyasa da ‘yan baranda a taron siyasa ko duk wata huldar siyasa da suka yi kokarin ta da rikici.

“Mun kuma kuduri aniyar daukar kwararan matakai da za su dakile kai hare-hare kan kadarorin INEC a fadin kasar nan.

“Muna gargadi da kakkausar murya a matsayinmu na jami’an tsaro da ‘yan siyasa da mu yi magana da murya daya don yin tir da tashe-tashen hankula na siyasa,” in ji shi.

Babban Sufeton ’Yan sandan ya ce shugabannin jam’iyyun siyasa na da muhimmiyar rawar da za su taka wajen kawar da ra’ayin siyasa, barazana, tashe-tashen hankula da sauran munanan dabi’u a tsarin dimokuradiyya.

Ya yi kira ga shugabannin jam’iyyun siyasa da su jajirce wajen nuna kyawawan halaye na jagoranci da kuma raba kawunansu a bainar jama’a daga ayyukan bata-gari da tashe-tashen hankula na siyasa.