✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnoni da Kwamitin Amintattun APC sun sa labule

Tsohon Shugaban APC na Kasa, Adams Oshiomhole na daga cikin mahalarta zaman

A halin yanzu gwamnoni shida na jam’iyyar APC na yin wata ganawar sirri tare da Shguaban Jam’iyyar na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu.

Tsohon Shugaban Jam’iyyar na Kasa kuma tsohon Gwamnan Jihar Edo, Adams Oshiomhole da mambobin kwamitin amintattun jam’iyyar na daga cikin mahalarta ganawar ta sirri a Sakatariyar Jam’iyyar da ke Abuja.

Gwamnonin da suka halarci zaman sun hada da Gwamnan Jihar Kano, Abduullahi Ganduje, Gwamnan Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar,  Simon Lalong na Jihar Filaot, Sani Bello na Jihar Neja da kuma Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa.

Har yanzu dai babu cikakken bayani game da ajandar ganawar a sirri, amma wasu majiyoyi na cewa za a yi ganawar ce domin shawo kan dambarwar da ta biyo bayan kafa kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.

Idan ba a manta ba a baya, Darakta-Janar na Kwamitin Yakin Neman Zaben, Gwamna Simon Lalong na Jihar Filato ya yi wata ganawa ranar Talata da mambobin kwamitinsa a Abuja.
%d bloggers like this: