Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya karbi bindigogi kirar AK47 guda 14 da albarusai 10,000 wadanda sojojin Najeriya suka kwato daga hannun ’yan bindiga.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ce kwamandan rundunar sojin kasa ta Najeriya da ake yiwa take Operation Hadarin Daji, Birgediya Janar Aminu Bande, shi ya mika bindigogin ga gwamnan a hedkwatar rundunar da ke Gusau.
Janar Bande, wanda kuma shi ne kwamandan Runduna ta 8 ta Sojin Kasa da ke Sakkwato, ya shaida wa gwamna cewa sakarunsa sun kuntata wa ’yan bindigar a cikin daji da ma hanyoyin da suke bi su gudu.
“Shi ya sa da dama daga cikinsu wadanda a da suka ki tuba yanzu suke kamun kafa a kan su zo su yi saranda a karkashin shirin samar da zaman lafiya na gwamnatin jiha saboda su kubuta daga ruwan azabar da sojoji suke yi musu”, inji Birgediya Bande.
Ya kara da cewa, “Za mu ci gaba da takun saka da wadannan bata-garin har sai kwanciyar hankali ya samu a fadin jihar da kewaye”.
- An samu saukin ta’addanci a Zamfara – Walin Sakajiki
- Kotun Koli ta yi watsi da bukatar duba hukuncinta kan Zamfara
Kwamandan ya jingina nasarorin da soji suka yi a kan hadin kai da suke samu daga jama’ar jihar, musmman wajen ba da bayanan da ke kaiwa ga tarwatsa bata-garin.
Gwamnan yay aba da kokarin sojojin sannan ya sanar da ba da gudunmawar Babura 190 don saukaka musu zirga-zirga a yankuna masu wahalar shiga, inda bata-gari ke neman mafaka.
Ya kuma ce nan ba da jimawa ba gwamnatin jihar za ta samar da karin abbaen hawa 200 ga hukumomin tsaro a jihar don taimaka musu kawar da miyagu.