Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya amince da naɗin Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a matsayin sabon Sarkin Katsinan Gusau.
Sakataren Gwamnatin Zamfara, Malam Abubakar Mohammad Nakwada ne ya bayyana haka a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Suleman Ahmad Tudu ya fitar a Talatar nan.
Sanarwar ta ce an yi amfani da dokoki da tanade-tanaden doka ne wajen amincewa da naɗin wanda masu zaɓen sarkin masarautar suka zaɓa.
Gwamna Lawal ya taya sabon sarkin murna, sannan ya yi kira gare shi da ya yi koyi da magabatansa, musamman ganin shi tsatson Malam Sambo Ɗan Ashafa ne.
Ya kuma yi kira ga sabon sarki ya dage wajen kira da samun haɗin kai da ci gaban masarautar Gusau da jihar, da ma ƙasar baki ɗaya.
Alhaji Abdulkadir zai ɗare karagar ne a matsayin Sarki na 16 na masarautar, inda zai maye gurbin mahaifinsa, Marigayi Mai martaba Dr. Ibrahim Bello, wanda ya rasu a ranar 25 ga watan Yulin 2025.
Sabon sarkin ne babban ɗan marigayin, kuma kafin naɗa shi sarki, shi ne Bunun Gusau.
Ana iya tuna cewa, a Juma’ar makon jiya ce aka samu rahoton rasuwar Sarkin Katsinan Gusau, Dokta Ibrahim Bello yana da shekara 71 da haihuwa.
Sarkin ya rasu ne a daren Juma’a 24 ga watan Yulin 2025 bayan doguwar jinya a wani asibiti da ke Abuja, babban birnin Nijeriya.
Sanarwar da gwamnatin Zamfarar ta fitar ta ce: “Rasuwar mai martaba babban rashi ne ga Jihar Zamfara da ma daukacin Arewacin Nijeriya.”
Gwamna Dauda Lawal ne ya jagoranci jana’izar sarkin a Babban Masallacin Juma’a na Kanwuri da ke birnin Gusau.
A watan Maris na 2015 aka naɗa marigayi Dokta Ibrahim Bello a matsayin sarkin Gusau na 15, inda ya maye gurbin ɗan’uwansa Alhaji Muhammad Kabiru Danbaba bayan rasuwarsa.
Marigayin ya bar mata da ’ya’ya sama da 20.