✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Yobe ta dauki ’ya’yan Sheikh Goni Aisami aiki

Gwamna Jihar Yobe, Mai Buni, ba da umarnin daukar ’ya’yan fitaccen malamin da sojoji suka kashe, Sheikh Goni Aisami, aiki a gwamnatin jihar.

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Buni, ba da umarnin daukar ’ya’yan fitaccen malamin da sojoji suka kashe, Sheikh Goni Aisami, aiki a gwamnatin jihar.

Gwamna Buni ya ba da umarnin daukar aiki kai tsaye ga biyu daga cikin ’ya’yan marigayin.

Gwamna Buni ya ba da umarnin ne a ranar Talata lokacin da iyalan marigayin suka ziyarce shi domin nuna godiyar su bisa yadda ya damu da su iyalan.

Buni ya tabbatar da cewa gwamnati za ta tabbatar da gudanar da bincike kan lamarin mutuwar malamin.
Ya kuma ba da tabbacin gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa ’yan uwan marigayin dangane da wannan babbar asarar da aka yi.

Malam Ibrahim Aisami, wanda ya yi magana a madadin ’yan uwa, ya nuna jin dadinsa da sakon ta’aziyya da ziyarar da wata babbar tawagar gwamnati ta kai domin jajanta wa iyalan.

Ya ce ba da wannan aikin zai rage wa iyalansu wahala sakamakon rasuwar malamin.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne wasu mutane biyu da ake zargin sojoji ne suka kashe Sheikh Aisami kan hanyar sa na dawowa gida daga Kano.

A halin da ake ciki, ’yan sanda sun kama wadanda ake zargin yayin da rundunar sojin ta sanar da cewa ta fara gudanar da bincike a kan lamarin domin fitar da cikakken bayani kuma duk wanda aka samu da hannu zai fuskanci hukuncin da dace da shi dai-dai da dokar kasa.