✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Yobe ta dauki matasa 3,196 aiki cikin shekaru biyar

Yobe za ta karbi bakuncin gasar wasannin shiyyar Arewa maso Gabas a wannan shekarar ta 2024.

Gwamnatin Yobe ta dauki kimanin matasa 3,196 aiki a jihar a cikin tsawon shekaru biyar da suka gabata.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Kwamishinan Matasa, Wasanni da Ci gaban Jama’a, Alhaji Barma Shettima a wata hira da manema labarai a Damaturu, babban birnin jihar.

Ya bayyana cewar, wadanda aka dauka aiki a lokacin gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni tun daga shekarar 2019, sun kasance masu digiri, takardar shaidar ilimi ta kasa (NCE) da kuma masu kwalin Difloma.

Barma ya zayyana bangarorin da aka dauki matasan aikin da suka hada da bangaren kiwon lafiya musamman likitoci da masu hada magunguna, ungozoma, ma’aikatan jinya da kuma bangaren dakin gwaje-gwaje.

Kwamishinan ya yi nuni da cewa, an dauki ma’aikatan ne domin a karfafa wa matasa gwiwa da kuma rage zaman kashe wando da ke bude kofar aikata miyagun laifuka da sauran munanan dabi’u a jihar.

Ya ce gwamnatin ta kuma nada matasa a matsayin shugabannin hukumomin gwamnati da dama da suka hada da hukumar ba da tallafin karatu ta Yobe, bankin bada rancen kudade na Yobe, hukumar bayar da agajin gaggawa ta Yobe da kuma hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta Yobe.

Ya bayyana cewa, “An kuma horar da matasa da dama a fannin sana’o’i daban-daban kamar dabarun noman zamani, kiwon dabbobi da sauransu.

“Manufar wannan gwamnati ita ce samar da yanayi mai kyau ga matasa don su rika gudanar da ayyuka masu ma’ana domin ci gaban jihar da kasa baki daya.

Shettima ya bayyana kafa dokar kare hakkin yara a jihar a matsayin daya daga cikin manyan nasarorin da ma’aikatar ta samu.

Ya ce, domin aiwatarwa ba tare da wata matsala ba, an riga an horar da masu ruwa da tsaki kan yadda za su wayar da kan jama’a kan bukatar bin dokar da ake fassarawa da harsunan gida.

A bangaren wasanni, Shettima ya bayyana cewa Yobe za ta karbi bakuncin gasar wasannin shiyyar Arewa maso Gabas a wannan shekarar ta 2024, yana mai cewa nan ba da jimawa ba za a fitar da cikakkun bayanai akan hakan.

Kwamishinan ya ce Gwamna Buni ya ba da umarnin cewa wasannin kokawar gargajiya da  wasan langa da sauran wasanni a inganta su tare da karfafa wa matasa gwiwa akan hakan.

Ya ce tuni shirye-shirye sun kai ga inganta filin wasa na 27 Agusta da ke Damaturu zuwa matsayin filin wasa na kasa da kasa, inda ya ce za a kuma kara inganta filin wasa na garuruwan Geidam, Potiskum, Gujba da Nguru.