✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Tinubu ta yi wa Sarki Sanusi raddi

Sarkin Kano na 16 ya furta kalaman cewa ba zai taimaki Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ba.

Gwamnatin Tarayya ta yi wa Sarki Muhammadu Sanusi II raddi tana mai cewa duk da ba ya tare da ita, akwai buƙatar ya ajiye son rai da nuna ɓangaranci ya mayar da hankali kan buƙatun ’yan Nijeriya.

Aminiya ta ruwaito cewa, a yayin wani taron tunawa da fitaccen lauyan nan ɗan gwagwarmaya, Cif Gani Fawehinmi da ya gudana ranar Laraba a Jihar Legas, Sarkin Kano na 16 ya furta kalaman cewa ba zai taimaki Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ba.

A yayin gabatar da jawabi, Sarki Sanusi II ya ce ba zai bai wa Gwamnatin Tinubu kowacce shawara da sunan taimako ba dangane da halin da ƙasar ta tsinci kanta ta fuskar tattalin arziki.

A cewar Sarkin, zai iya yin tsokaci kan wasu batutuwa da suka shafi Nijeriya da hasashen abin da zai iya faruwa da kuma shawarar yadda za a iya kaucewa hakan.

Sai dai a cewarsa, ba zai yi hakan ba, domin muddin ya ba da wata shawara tamkar ya taimaki gwamnatin ta Tinubu ce kuma a halin yanzu ba shi da niyyar taimakonta.

A cikin wata sanarwa ta mayar da martani da Ministan Labarai da Wayar da kan Al’umma, Mohammed Idris ya fitar, gwamnatin ta nuna takaicinta “kan yadda matakan da take ɗauka waɗanda ƙwararru a duniya suka amince da su, ciki har da shi Sarki Sanusi, a yanzu yake sukar su saboda ba ya tare da gwamnatin.

“Gwamnatin Tinubu ta yarda da cewa Sanusi, da ma duk wani ɗan Najeriya na da damar faɗin ra’ayinsa ta hanyar jinjina ko kuma suka kan yadda ake tafiyar da gwamnati.

“Sai dai abin mamaki ne a ce shugaba, musamman wanda ya fito daga ɓangaren da ke girmama faɗin gaskiya, da adalci, zai fito fili ya nuna cewa yana ƙin faɗin gaskiya saboda son rai da kuma tunanin ana ƙinsa.

“Sannan kuma gwamnatin nan ba ta buƙatar amincewar Sarki Sanusi kan muhimman manufofinta, waɗanda a halin yanzu sun kai wata gaɓa da wajibi ne a ɗauki irin waɗannan tsauraran matakai da tsare tsare domin magance matsalolin tattalin arziki, waɗanda kuma a yanzu sun fara samar da ci gaban da ake buƙata.

“Gwamnati na ɗaukar matakan da za su kawo sauyi ne ba don suna da sauƙi ba, sai dai domin suna da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da makoma mai kyau da kuma cigaba mai ɗorewa ga ƙasar, kamar yadda Sarki Sanusi ya yi ta fafutukar ganin an samar,” in ji sanarwar.

A cewar gwamnatin, “sake gina Najeriya na buƙatar haɗin kai, mayar da hankali da kuma sadaukarwa daga dukkanin masu ruwa da tsaki, kuma a matsayinmu na gwamnati, muna buƙatar shugabbanin al’umma su gujewa kalaman da za su kawo cikas ga amincewar da al’umma ke da shi a kanmu.”

Sanarwar ta ƙara da cewa “wannan wani lokaci ne mai muhimmanci a ƙasar, kuma abin da ake buƙata shi ne haɗin gwiwa ba rarraba hankali ba.

“Gwamnatin Bola Tinubu ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba kan manufofinta na kai Nijeriya ga tudun mun tsira, kuma kofarta a buɗe take domin tattaunawa masu muhimmanci da masu ruwa da tsaki, a yayin da kuma take tsayin daka kan sanya buƙatun Nijeriya sama da komai.”