✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Tarayya za ta sa Almajirai 11,000 a makaranta

Ministan ya ce hakan zai taimaka wajen inganta rayuwar Almajiran ta hanyar samun ilimin zamani.

Gwamnatin Tarayya na shirin sanya Almajirai sama da 11,000, da aka gano a Abuja a makarantu nan da watan Satumban 2024.

Shiri na da nufin bai wa Almajirai ilimin boko da kuma kyautata rayuwarsu.

Ƙaramin Ministan Ilimi, Dokta Yusuf Sununu ne, ya bayyana wannan yayin ziyarar da ya kai Makarantar Fasaha ta Birnin Tarayya da ke Karshi.

Dokta Sununu, ya sanar da cewa an soke kwangilar ginin makarantar fasahar a Jihar Kebbi sakamakon jinkiri, amma an sake bai wa wani kamfani kwangilar kammala aikin.

Kazalika, ya ce shirye-shirye na ci gaba na kammala ginin makarantar fasahar a Jihar Bayelsa, biyo bayan soke kwangilar da aka yi da kamfanin da ya fara aikin.

Ya yi kira ga jihohin da suka kammala ginin makarantun fasahar da su bai wa Gwamnatin Tarayya sunayen malamai 75 da suka ɗauka don fara ba su horo.

Aikin Makarantar Fasaha, wanda UBEC da KOICA suka tallafa aka samar, na da nufin ƙara samar wa malamai ƙwarewa a fannin Kimiyya da Fasaha da inganta samun kayan koyarwa masu inganci.

Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman, ya jaddada sauyin da ake yi zuwa koyarwar zamani da fasaha don inganta harkar ƙirƙire-ƙirƙire da tunanin ɗalibai.