Gwamnatin Tarayya ta shirya karya farashin shinkafa, inda za ta fara sayar da kowane buhu a kan Naira 40,000 a faɗin Najeriya.
Gwamnatin Tarayya ta ce za ta sayar da shinkafarta kan Naira dubu 40,000, saɓanin yadda farashinta yake a kasuwa na Naira dubu 80 da ’yan kai.
Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris ne, ya bayyana cewa, babban maƙasudin ɗaukar wannan matakin shi ne samar da walwala ga talakan Najeriya wanda ke ci gaba da kokawa kan tsadar rayuwa.
Ministan ya ƙara da cewa, tuni gwamnati ta kafa kwamiti na musamman wanda zai tsara yadda za a sayar da shinkafar a jihohin ƙasar nan.
Kazalika, ya bayyana cewa za a tabbatar cewa, babu wanda ya sayar da buhun shinkafar sama da farashin Naira dubu 40,000.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zanga-zanga kan yunwa da matsin rayuwa a ƙasar nan a ranar 1 ga watan Agusta domin bayyana wa gwamnati ɓacin ransu.
Sai dai a gefe guda, gwamnatin ta yi tir da shirin gudanar da zanga-zangar, inda ta ce tana yin mai yiwuwa don daidaita al’amura ta yadda talaka zai ji daɗi.