✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Tarayya za ta biya Naira biliyan 88 ga raunanan yakin Biyafara

Gwamnatin Tarayya ta amince za ta biya diyyar Naira biliyan 88 ga wadanda suka jikkata a yayin yakin Biyafara. Wannan batu ya biyo bayan amincewa…

Gwamnatin Tarayya ta amince za ta biya diyyar Naira biliyan 88 ga wadanda suka jikkata a yayin yakin Biyafara.

Wannan batu ya biyo bayan amincewa da hukuncin kotun jin koken al’umma ta kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin kasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS), inda Naira biliyan 50 za a mika su ga al’ummar da yakin ya raunata a jihohi 11 na Kudu Maso Gabas da Kudu Maso Kudu da kuma Arewa ta tsakiya; a yayin da sauran Naira biliyan 38 za a yi amfani da su wajen kawar da bama-bamai da sauran muggan makaman da aka daddasa a yankunan da kuma sake gina makarantu da kotu-kotu da majami’u da masallatai da sauransu a yankunan da yakin ya shafa.

A lokacin da yake karanta hukuncin kotun, Mai shari’a Friday Chijioke Nwoke ya bayyana cewa ana sa ran Gwamnatin Tarayya za ta biya Naira biliyan 50 din zuwa bankin UBA ga lauyan al’ummar da abin ya shafa, mai suna Cif Agwuocha Chukwudibia. Sai kuma cikon Naira biliyan 38 da za a biya a wani asusun ajiya na bankin UBA, mallakin kamfanin Deminers Concept Nigeria Limited, wanda zai yi aikin share wuraren da yakin ya shafa da kuma aikin gine-ginen majami’u da masallatai da makarantu da sauransu, kamar yadda aka tsara a baya.

Haka kuma, ana sa ran Gwamnatin Tarayya za ta kafa wata cibiya domin kula da wadanda yakin ya lahanta a yankin Kudu Maso Gabas. Haka kuma, domin ganin an tafiyar da dukkan kudurorin cikin nasara, gwamnati za ta kafa kwamiti mai karfi, wanda zai kunshi dukkan wakilan masu ruwa da tsaki, domin aiwatar da dukkan bukatun da aka zayyana a hukuncin.