✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Tarayya ta umarci MTN ya biya bashin harajin Dala biliyan 2

Gwamnatin Tarayya ta umarci Kamfanin MTN ya biya bashin harajin Dala biliyan biyu wanda ya yi daidai da Naira biliyan 700  Wannan matakin da Gwamnatin…

Gwamnatin Tarayya ta umarci Kamfanin MTN ya biya bashin harajin Dala biliyan biyu wanda ya yi daidai da Naira biliyan 700 

Wannan matakin da Gwamnatin Tarayya ta dauka na zuwa ne kwana shida bayan Babban Bankin Najeriya ya bukaci kamfanin ya dawo da Dala biliyan 8.13 da ya fitar daga kasar ba bisa ka’ida ba.

A nasa bangaren, mai magana da yawun Kamfanin MTN, Funsho Aina ya ce ba a bin kamfanin bashin haraji, domin kamfanin ya biya Dala miliyan 700, kimanin Naira biliyan 214 ke nan, “Lura da cikakken binciken da muka gudanar, mun yi imanin cewa mun biya dukan harajin Kamfanin MTN da ake magana ana bin kamfanin,” inji Aina.

A kwanaki takwas da suka wuce, Babban Bankin Najeriya ya umarci MTN ya dawo da wasu kudade da ya fitar zuwa kasar Afirka ta Kudu ba bisa ka’ida ba, kuma ya ci tarar bankunan Diamond da Stanbic IBTC da Citi da Standard Chattered da suka taimaka wa kamfanin wajen fitar da kudaden. 

Saboda matsalolin da MTN ke fuskanta, hannun jarin kamfanin ya fadi da kashi 20 cikin 100 c mako guda kamar yadda jaridar Premiun Times ta ruwaito.

Kamfanin MTN ya ce ofishin Ministan Shari’a na Najeriya ya yi lissafin cewa ana bin kamfanin bashin Dala biliyan biyu na harajin shigo da kayayyaki da kuma biyan kudi ga ’yan kwangila cikin shekara 10 da suka wuce.

Bayannin harajin a kan MTN ya fito ne a cikin wata sanarwar da ta yi karin bayani game da Dala biliyan 8.1 da Babban Bankin Najeriya ya ce an fitar daga kasar ba bisa ka’ida ba.

A shekarar 2015 Hukumar Sadarwa ta Najeriya ta ci tarar kamfanin MTN wanda asalinsa na kasar Afirka ta Kudu ne Dala biliyan biyar don kin bin umarnin gwamnati na katse layukan mutum miliyan biyar da ba a yi musu rijista ba, sannan daga baya aka rage tarar zuwa Dala biliyan 1.7.

Fiye da ’yan Najeriya miliyan 50 ne ke amfani da MTN, kuma kashi 30 cikin 100 na harkar cinikayyar kamfanin na gudana ne a Najeriya.