✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Tarayya ta soki Amurka kan matsayinta a kan kungiyar IPOB

Gwamnatin Tarayya ta bayyana nadamarta kan matsayin da Amurka ta dauka dangane da ayyana kungiyar IPOB cikin jerin kungiyoyin ta’addanci a kasar. Ministan Yada Labarai…

Gwamnatin Tarayya ta bayyana nadamarta kan matsayin da Amurka ta dauka dangane da ayyana kungiyar IPOB cikin jerin kungiyoyin ta’addanci a kasar.
Ministan Yada Labarai na Najeriya da Al’adun Gargajiya, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana matsayin gwamnatin a daren jiya a birnin Landan a tattaunawar da gidan rediyon BBC ya yi da shi a shirinsa mai taken “Fuskantar Nahiyar Afirka”.
Ministan wanda ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta yi daidai da ta aiyana kungiyar IPOB a matsayin kungiyar ta’addanci.
Ya bayyana rashin jindadinsa dangane da jayayyar da kasar Amurka take yi da matsayin da Najeriya ta dauka kan kungiyar.