Gwamnatin Tarayya ta shiga tsakani a dambarwar da ke faruwa a Jihar Kaduna inda ta kira ga Gwamna Nasir El-Rufai da Shugaban Kungiyar Kwadago ta Kasa, Ayuba Wabba tare da takwaransa na TUC, Quadri Olaleye, da su tsagaita wuta a cikin gaggawa.
Ministan Kwadago da Samar da Ayyuka, Chris Ngige, ta hannun mai magana da yawun Ma’aikatar, Charles Akpan, ya gargadi bangarorin biyu da kada su bari lamarin ya zama wanda ba za a iya shawo kansa ba.
- An yi garkuwa da alkali a cikin kotu
- Dan sanda ya mayar da N1.2m da ya tsinta a Kano
- Matakan nada Khalifan Tijjaniyya — Sheikh Dahiru
- Matakan soyayya da bayaninsu dalla-dalla
“Ba mu da masaniyar abin da ke faruwa a Jihar Kaduna. Batu ne na kwadago wanda ya rikide zuwa yajin aiki na kasa da kungiyoyin kwadago da takwarorinsu suka shiga.
“Muna fata da addu’ar kada Gwamnan Kaduna ya kara dagula lamuran zuwa matakin da ba za a iya shawo kansa ba.
“Muna kuma yin kira ga shugabannin cibiyoyin kwadagon da su sauka daga kujerar na-kin da suka hau domin ba da damar tattaunawa.
“Ma’aikatata tana shiga tsakani kan lamarin don haka ta yi kira ga bangarorin da ke husumar da su ba zaman lafiya dama,’’ inji sanarwar.