Gwamnatin Tarayya ta sake rage farashin mai zuwa N121.50
Gwamnatin tarayya ta sanar da kara rage farashin man fetur zuwa N121.50 a kan kowacce lita.
Hukumar da ke kula da farashin mai ta Kasa (PPPRA) wacce ita ce ke da alhakin daidaita farashin ce dai ta sanar da ragin daga N123.5 da ake sayarwa yanzu haka kan kowacce lita.
• An rage farashin man fetur daga Naira 145 zuwa 125
• An sake rage farashin man fetur a Najeriya
Wannan sabon umarnin dai na kunshe ne a cikin wata wasika da hukumar ta raba wa kungiyar masu sayar da man da ke dauke da kwanan watan 31 ga watan Mayu.
Rahotanni dai na nuni da cewa ragin ya biyo bayan faduwa warwas da farshin danyen man ya yi a kasuwar duniya sakamakon annobar cutar coronavirus.
Wannan dai shi ne karo na uku da gwamnatin tarayya ta ke rage farashin man a shekarar da mu ke ciki inda a ranar 18 ga watan Maris din da ya gabata ta sanar da rage farashin daga N145 zuwa N125 a kan kowacce lita.
Hakazalika, ranar 31 ga watan dai na Maris gwamnatin ta sanar da kara rage farashin zuwa N123.50.