✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Gwamnatin Tarayya ta mayar da Arewa maso Gabas saniyar ware’

An mayar da Arewa maso Gabas saniyar ware ta fuskar kai ayyukan more rayuwa na Gwamnatin Tarayya zuwa yankin.

Gwamnonin Arewa maso Gabashin Nijeriya sun yi ƙorafi kan wasu abubuwa da ke ci musu tuwo a ƙwarya dangane da yadda Gwamnatin Tarayya ta mayar da yankinsu saniyar-ware ta fuskar rabon manyan ayyuka.

Gwamnonin sun bayyana damuwar ce a cikin wata sanarwa da suka fitar bayan taron Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabas (NEGF) da suka gudanar ranar Asabar a Bauchi.

A cikin sanarwar, gwamnonin ƙarƙashin jagoranci shugaban ƙungiyar, Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno, sun bayyana abubuwa da dama da suke damun yankin na Arewa maso Gabas inda suka ce akwai buƙatar gwamnatin tarayya ta sa baki a ciki.

Daga cikin ƙorafe-ƙorafen da suka yi akwai batun yadda ake mayar da yankin saniyar ware ta fuskar kai ayyukan more rayuwa na gwamnatin tarayya zuwa yankin.

Sun bayyana cewa sun shafe shekaru suna fama da tituna marasa kyau da kuma yadda layin dogo wanda ya tashi daga Maiduguri zuwa Enugu ya lalace wanda suka ce hakan ba ƙaramin koma-baya bane ga tattalin arziƙinsu.

Haka kuma sun yi ƙorafi kan cewa yankin ba a saka shi a sabon shirin nan na sauyi daga fetur zuwa CNG ba da za a yi a Nijeriya.

“Wannan ƙungiyar na nuni da rashin jin dadi dangane da rashin lantarkin da ake fama da shi a yankin na tsawon wata guda da kuma halin ko-in-kula da TCN ke nunawa domin maganace matsalar wadda ke da muhimmanci ga tsaro da ci gaban ƙasa,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Gwamnonin sun buƙaci gwamnatin tarayyar kan ta bayar da umarni ga kamfanin dakon wutar lantarki na TCN kan ya yi gaggawar magance wannan matsalar.

Ƙungiyar ta kuma jaddada cewa matsalolin sauyin yanayi da na muhalli na daga cikin matsalolin da suke damun yankin inda gwamnonin suka gode wa juna dangane da matakan da suke ɗauka domin gyara muhalli amma kuma sun yi kira da a haɗa kai domin ɗaukar matakai masu ɗorewa na yaƙi da kwararowar hamada.

“Ƙungiyar na kira ga Hukumar Kula da Arewa Maso Gabashin Nijeriya da ta riƙa tuntuɓa a abubuwa da ayyukan da take yi.

“Ƙungiyar na kira ga NEDC da ta yi aiki tare da jihohin yankin domin samun ci gaba ta fannin makamashi don buɗe kofofin da ke rufe ta wannan fannin a yankin da kuma rage wa jama’ar yankin matsalolin da suke fuskanta,” in ji sanarwar.

Haka kuma sakamakon matsalolin da ake fuskanta na ƙarancin abinci saboda yaƙin Ukraine da sauyin yanayi da rashin yabanya a gonaki, gwamnonin sun amince su ci gaba da zuba jari ta ɓangaren noma.

Gwamnonin sun ce za su taimaka wa manoma samun iri da takin zamani a farashi mai rahusa.