Gwamnatin Tarayya ta amince da bukatar haramta wa baki ’yan kasashen waje sayen amfanin gona kai tsaye daga manoma ko kuma amfani da wakilansu.
Wannan dai na zuwa ne a matsayin wani yunkuri na bunkasa harkokin kasuwanci a cikin gida.
- ‘Sojoji sun kashe masu zanga-zanga 13 a Chadi’
- Pochettino ya caccaki alkalancin wasan PSG da Real Madrid
Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Zuba jari, Otunba Adeniyi Adebayo ya bayyana matakin bayan taron Majalisar Zartarwa wanda Matamakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta a ranar Laraba.
Adebayo ya ce sakamakon amincewa da wannan shirin, ’yan kasuwar cikin gida ne kawai da ke da lasisin yin cinikin amfanin gonaki kai tsaye daga manoma domin sayarwa baki ’yan kasashen waje.
Ministan ya ce wannan mataki zai toshe kofar cutar manoman da bakin ke yi wajen karbe amfanin gonakin su da ’yan kudi da ba su taka kara sun karya ba.