Yayin da ’yan Najeriya ke shirin gudanar da zabukan Shugaban kasa da na ‘yan Majalisar Tarayya a ranar Asabar, Gwamnatin Tarayyar ta ba da umarnin rufe dukkan iyakokin kan tudu na kasar.
Shugaban Hukumar Shige da Fice ta Najeriya, NIS, Isah Idris Jere shi ne ya bayyana haka a wata sanarwar da ya fitar da Yammacin Alhamis a birnin tarayya Abuja.
- Sheikh Dahiru Bauchi ya karyata sautin goyon bayan Atiku
- Sojoji sun kashe ’yan bindiga 5, sun kwato makamai a Kaduna
Shugaban NIS ya ce za a rufe kan iyakokin ne daga ranar Asabar zuwa Lahadi.
Sanarwar ta ce, “Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe duk iyakokin kasa daga karfe 12 na safiya a ranar Asabar 25 ga watan Fabrairun shekarar 2023 zuwa karfe 12 na safiya a ranar Lahadi, 26 ga watan Fabrairun shekarar 2023.
“A don haka sanarwar ta ce, duk wani kwamanda ma’aikatar musamman wadanda ke jihohin da ke kan iyaka su tabbatar da ganin an bi umarnin daidai-wa-deda.”