✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun hutun Babbar Sallah

An buƙaci musulmi da su yi amfani da wannan damar wajen yi wa ƙasar nan addu’o’in zaman lafiya.

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin da Talatar makon gobe a matsayin ranakun hutu domin shagalin bikin Babbar Sallah ta bana. 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babbar sakatariya a ma’aikatar harkokin cikin gida, Dokta Aishetu Ndayako ta fitar a wannan Juma’ar.

Dokta Ndayako ta ambato Ministan Harkokin Ciki Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo yana taya daukacin al’ummar musulmi na gida da na ketare murnar wannan rana ta idin layya.

Ministan ya kuma yi kira ga al’ummar musulmi da su ci gaba da riko da kyawawan halaye na zaman lafiya, kyautatawa da sadaukarwa kamar yadda Manzon Tsira, Annabi Muhammad (SAW) ya yi wasici da su.

Tunji-Ojo ya buƙaci musulmi da su yi amfani da wannan damar wajen yi wa ƙasar nan addu’o’i na zaman lafiya da haɗin kai.

Kazalika, ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare rayuka da dukiyoyin ’yan Nijeriya.