✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnatin Taliban na rokon kasashen Musulmi su aminta da ita

Fira Ministan kasar Afhghanistan, Mohammad Hassan Akhund, ya yi kira ga kasashen Musulmi da su aminta da gwamnatin Taliban tare da yin aiki tare da…

Fira Ministan kasar Afhghanistan, Mohammad Hassan Akhund, ya yi kira ga kasashen Musulmi da su aminta da gwamnatin Taliban tare da yin aiki tare da ita a hukumance.

Ya yi kiran ne a ranar Laraba, wata biyar bayan Taliban ta karbe gwamnati a kasar, shekara 20 bayan sojojin kawancen Amurka sun hambarar da gwamnatinta a kasar.

“Ina kira ga daukacin kasashen Musulmi su zama a sahun gaba wajen aminta da gwamnatin Taliban a hukumance. Hakan zai taimaka mana wajen samun ci gaba da wuri,” inji shi.

Mohammad Hassan Akhund ya bayyana wa wani taron manema labarai a Kabul babban birnin kasar cewa Afghanistan tana cikin matsananciyar matsalatar koma-bayan tattalin arziki.

A halin yanzu dai babu wata kasa da ta amince da gwamnatin Taliban a hukumance, a yayin da kasashen Yamma ke bibiyar yadda Taliban din za ta gudanar mulkin kasar a wannan karon.

Kasashen Yamma dai na ganin a mulkin Taliban na baya (1996 zuwa 2021) kungiyar ta rika cin zali da cin zarafi sosai gami da tsakura wa mutanen kasar.

A halin yanzu dai kasashen da ke neman kai agaji Afghanistan suna cikin tsaka-ai-wuya, saboda yawancin jami’an gwamantin wucin gadin da Taliban din ta nada suna cikin jerin mutanen da aka sanya wa takunkumi a kasashen duniya.

Amma Akhund ya ce, “Ba ma bukatar taimako daga wani. Ba don jami’an gwamnati muke yi ba, don jama’a muke yi,” yana nufin neman aminta da gwamnatinsu.

Ya kara da cewa Taliban ta cika duk sharudda da suka kamata na tabbatar da dawowar zaman lafiya a kasar.
%d bloggers like this: