✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Sojin Myanmar Ta Tsare Tsohuwar Jakadiyar Birtaniya

Gwamnatin sojin kasar Myanmar ta tsare tsohuwar Jakadiyar Britannia a kasar, Vicky Bowman.

Gwamnatin sojin kasar Myanmar ta tsare tsohuwar Jakadiyar Britannia a kasar, Vicky Bowman a gidan yari.

Wata majiyar diflomasiya ta ce an kama Vicky Bowman ne tare da mijinta dan asalin kasar a Yangoon, babban birnin kasar a ranar Alhamis.

Vicky ita ce Jakadiyar Britannia a Myanmar daga shekarar 2002 zuwa 2006; bayan ta kasance mai kula da ofishin jakadancin a matsayin Babbar Magatakarda daga 1990 zuwa 1993.

Rahotanni daga kafofin yada labarai na kasar na cewa ana tsare da su ne a Gidan Yarin Insein a Yangoon.

Gwamnatin Mulkin soji ta kasar ba ta ce komai ba, dangane da tsare ta ba, amma ana kyautata zaton za a a tuhume su ne da keta dokokin shige da fice na kasar.