Gwamnatin sojin kasar Myanmar ta tsare tsohuwar Jakadiyar Britannia a kasar, Vicky Bowman a gidan yari.
Wata majiyar diflomasiya ta ce an kama Vicky Bowman ne tare da mijinta dan asalin kasar a Yangoon, babban birnin kasar a ranar Alhamis.
- Shugaban ’yan sandan Japan ya yi murabus kan kashe tsohon Fira Minista
- Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 6 a kasuwar ’yan ta’adda
Vicky ita ce Jakadiyar Britannia a Myanmar daga shekarar 2002 zuwa 2006; bayan ta kasance mai kula da ofishin jakadancin a matsayin Babbar Magatakarda daga 1990 zuwa 1993.
Rahotanni daga kafofin yada labarai na kasar na cewa ana tsare da su ne a Gidan Yarin Insein a Yangoon.
Gwamnatin Mulkin soji ta kasar ba ta ce komai ba, dangane da tsare ta ba, amma ana kyautata zaton za a a tuhume su ne da keta dokokin shige da fice na kasar.