Gwamnatin Jihar Ondo ta ba ma’aikatan Jihar wa’adin mako biyu su yi allurar rigakafin COVID-19.
Umarnin na kunshe ne a cikin wata wasika dauke da sa hannun Babban Sakatare mai kula da ma’aikatan gwamnatin Jihar, Mista O. J. Afolabi ya fitar.
Gwamnatin ta ce daga yanzu ya zama wajibi ma’akatanta su nuna katin shaidar cewa an yi musu rigakafin kafin su amfana da wasu abubuwan na gwamnati.
- Maharan da suka kashe kanin Sowore sun sace mutum 5
- Kotu ta tsare matar da ta ba da daki ana lalata a Zariya
Afolabi ya ce matakin na cikin irin yunkurin da gwamnatin Jihar ke dauka don dakile cutar a Jihar.
“Sakamakon sake barkewar cutar a karo na uku ta hanyar sabuwar nau’in Delta, ya zama wajibi gwamnati ta umarci dukkan ma’aikatanta da su je su yi rigakafin cutar nan da mako biyu masu zuwa daga ranar da aka fitar da wannan sanarwar,” inji Afolabi.
Gwamnatin ta kuma ja kunen ma’aikatan kan bin cikakkun ka’idojin kariya daga cutar yayin yin rigakafin.
Sai dai yanzu haka ’yan Najeriya na nuna mabambantan ra’ayoyi kan matakin tilasta wa mutanen yin rigakafin.
A Jihar Edo alal misali, yunkurin Gwamna Godwin Obaseki na tilasta wa mutane su karbi rigakafin ya hadu da tirjiya a Jihar, duk da cewa ya ce yana nan daram a kan bakarsa.
Yanzu haka dai Gwamnatin Tarayya ita ma na duba yuwuwar tilasta mutane su karbi rigakafin, a daidai lokacin da Najeriya kamar sauran kasashen duniya ke fuskantar sake barkewar cutar a karo na uku.