✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Nasarawa na da fuskar mutane amma akidarta ba ta mutane ba ce – Shugaban PDP

Bayan shekara biyu da kwace mulkin Jihar Nasarawa daga hannun Jam’iyyar PDP da tsohuwar Jam’iyyar CPC (yanzu APC) karkashin Gwamna Umar Tanko Al-Makura ta yi,…

Bayan shekara biyu da kwace mulkin Jihar Nasarawa daga hannun Jam’iyyar PDP da tsohuwar Jam’iyyar CPC (yanzu APC) karkashin Gwamna Umar Tanko Al-Makura ta yi, shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Mista Yunana Iliya, Kuyambanan Karu, ya ce gwamnatin jihar tana da fuskar mutane amma akidarta ba ta mutane ba ce domin ta kasa aiwatar da komai na ci gaban al’ummar jihar:

 

 

Aminiya: Yallabai lokacin zabe na kara kusaowa, wadanne shirye-shirye kuke yi don samun nasara?
Yunana Iliya: Shi dan siyasa a koyaushe a shirye yake don ya ci nasara. Yana iya kokarinsa ne ya ga ya jawo hankulan jama’a su ba shi goyon baya. Jam’iyyar PDP jam’iyya ce da ta kafu a nan Jihar Nasarawa. Jam’iyyar ce wace ko a tsakar dare aka kira ta za ta iya bayyana abin da ta sa a gaba. Kadan daga cikin shirye-shiryen da muke yi game da zabubbuka masu zuwa su ne za mu fara zagayawa garuruwa da kauyukan jihar nan mako mai zuwa inda za mu ziyarci mambobinmu, mu ga halin da suke ciki a bangaren siyasa mu kuma sanar da su shirye-shiryenmu game da zabubbuka masu zuwa.
Aminiya: Yaya za ka kwatanta gwamnatin Al-Makura da ta PDP da ya gada?
Yunana Iliya: Duk wanda ke da rai da idanu ba sai an gaya masa cewa ga shi-ga shi ba, ya san cewa kimanin shekara biyu da watanni, ba abin da gwamnati mai ci ta yi don ba gwamnatin jama’a ba ce. Gwamnati ne da ke da fuskar mutane amma akidarta ba ta mutane ba ce, domin daya daga cikin muhimman hakokin kowane gwamnati shi ne tabbatar da tsaro. Bayan rashin tsaro wannan gwamnati ba ta yin komai don inganta rayuwar al’ummarta. Kowa ya san cewa da fara aikin wannan gwamnati, an kori ma’aikata da dama da haka ya ja musu wahala sosai. Ga matasa kuma ba aikin yi, akwai abubuwa da daban-daban da gwamnati mai ci yanzu ta kasa yi da idan zan bayyana maka zan kwana ban gama ba. Amma a lokacin PDP kowa ya san cewa ba a taba yin fadace-fadace a kai a kai kamar yadda ake yi yanzu ba. Shi ya sa ka ga talakawan jihar nan ke fuskantar wahalhalu don idan zakuna biyu suna fada ciyawa ce ke shan wahala. Duk ayyuka da kake gani a jihar nan an yi su ne a lolacin PDP. Gwamnati mai ci yanzu ta zo ta tarar da su ne ba ita ta yi ba. Saboda haka gwamnatin PDP da suka shude sun yi ayyuka a jihar nan da ba za a iya kwatanta da wata gwamnati ba balle ta Al-Makura.
Aminiya: Me za ka ce game da rikcin Jam’iyyar PDP a matakin kasa?
Yunana Iliya: To ga wadanda ba su san me ake ciki a siyasar kasar nan ba ne suke cewa Jam’iyyar PDP ta rabu biyu. Amma mu da muke jam’iyyar mu san cewa PDP daya ce kuma shugabanta shi ne Alhaji Bamanga Tukur. Ba mu da wani shugaba bayansa. Dalili kuwa shi ne Kawu Baraje da ya fito yana cewa shi ne shugaban Jam’iyyar PDP, ya yi takarar shugaban PDP ne ? Ba zai yiwu don ka samu matsala da shugabanka sai ka mayar da shi fada kai ka zama sarki ba. A matsayinka na da gun mahaifinka kukan samu rashin jituwa, idan haka ya faru sai ka ce kai ne uba a wurin mahaifinka. Ka ga haka ba zai yiwu ba. Shugabanmu shi ne Dokta Bamanga Tukur uban jam’iyya kuma shi ne Goodluck Ebele Jonathan. Na san Bamanga Tukur, ya san ni, na san shugabannin PDP a kananan hukumomin jihar nan, sun san ni. Na san shugabannin PDP na ungwanni sun san ni. Saboda haka wasu mutane ne kawai daga cikinmu da ke so su yi kafar ungulu ga jam’iyyarmu don son ransu ke kokarin kawo rudani.
Aminiya: A karshe wane kira kake da shi ga ’ya’yan Jam’iyyar PDP da al’umma game da matsalar rashin tsaro da jihar nan ke fama da shi a halin yanzu?  
Yunana Iliya: Kiran da nake yi a kullum shi ne jama’a a yi hakuri da juna a kuma ba Jam’iyyar PDP kuri’u a zabubbuka masu zuwa don ita ce kawai za ta iya kawo karshen rigirgimun da ake fuskanta a jihar nan ta kuma samar musu da romon dimokuradiyya. Su kuma ’yan PDP kada su saurari wani ko wasu mutane da za su zo su rude su cewa su koma wata jam’iyya daban don kada su yi da-na-sani daga baya.