✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin May ta tsallake rijiya da baya

A shekaraniya Laraba ce gwamnatin Firayi Ministan Birtaniya Theresa May ta tsallake rijiya da baya daga kuri’ar rashin amincewar da gwamnatin, bayan da ta samu kuri’a…

A shekaraniya Laraba ce gwamnatin Firayi Ministan Birtaniya Theresa May ta tsallake rijiya da baya daga kuri’ar rashin amincewar da gwamnatin, bayan da ta samu kuri’a 325 yayin da masu son a kawar da gwamnatin suka samu kuri’a 306

Wannan yana zuwa ne kasa da kwana daya bayan da wakilan Majalisar Dokokin Birtaniya suka yi watsi da shirin Firayi Minista Theresa May bayan sun kada kuri’ar kin amincewa da yarjejeniyar da ta cimma da Kungiyar EU kan shirin gwamnatin kasar na ficewa daga Kungiyar Tarayyar Turai.

A yayn kada kuri’ar kan yarjejeniyar da Theresa May ta cimma da EU, ’yan majalisa 432 ne suka yi watsi da yarjejeniyar yayin da 202 suka goyi bayanta.

Jagoran Jam’iyyar Labour kuma Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar, Jeremy Corbyn ya ce “bahaguwar” gwamnatin May   ta rasa damar da za ta ci gaba da mulki a lokacin da aka shafe awa shida ana muhawara kan kudirinsa.Jam’iyyarsa ta ce ba ta yanke kaunar sake gabatar da bukatar sake kada kuri’ar yanke kauna ga gwamnatin Theresa May ba.

Da take mayar da jawabi bayan sakamakon kada kuri’ar Misis May ta ce za ta ci gaba da aiki don biyan bukatun al’ummar kasar kan kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta ficewa daga Tarayyar Turai.

A watan Disamban da ya gabata, May ta fuskanbore daga mambobin majalisar na jam’iyyarta, amma ta sha da kyar.

Shugaban Kungiyar Tarayyar Turai, Donald Tusk ya shawarci BIrtaniya ta ci gaba da zama a cikin kungiyar, bayan majalisar kasar ta yi fatali da daftarin Firayi Ministar na ficewa daga Turai.

A wani sako twitter da ya wallafa, Mista Tusk ya ce idan yarjejeniya ta ki samuwa, kuma babu wanda ya ke son ganin an cimma daidaituwa, to wa ke da zuciyar cewa ga shawara takamammiya.