✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Legas ta yi shirin ko-ta-kwana a daminar bana

Duba da sa’a 24  da aka kwashe ana kwarara ruwan sama tamkar da bakin kwarya  a Jihar Legas a karshen makon jiya, gwamnatin jihar ta…

Duba da sa’a 24  da aka kwashe ana kwarara ruwan sama tamkar da bakin kwarya  a Jihar Legas a karshen makon jiya, gwamnatin jihar ta kwantar wa mazauna garin hankula,  ganin yadda ta shirya wa ruwan saman na marka-marka ta hanyar yashe magudanan ruwa da tsabtace muhalli.
A wata sanarwa da kwamishinan muhalli na jihar ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata Babatunde Adejare, ya ce tuni gwamnatin Legas ta yi nisa a aikin yashe magudanan ruwa, musanman a yankunan da suka yi fama da ambaliyar ruwa a baya. Domin haka ne ya sanya su wayar wa jama’a kai bisa illar zubar da shara a magudanan ruwa
“Babu wani mutumin kwarai da zai ringa tushe magudanan ruwa,  kiraye-kirayen da muka yi ta yi a baya, mun yi ne don kyautatuwar rayuwar jama’a,” inji shi.
Kwamishinan ya ce gwamnantin jihar za ta rushe duk haramtattun  gine-ginen da aka yi a bisa magudanan ruwa, sannan duk wanda aka samu da toshe magudanan ruwa za a ladabtar da shi.