✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yanzu-yanzu: Gwamnatin Legas ta sassauta dokar hana fita

Yanzu dokar hana fita ta koma daga karfe 6 na yamma zuwa karfe 8 na safe a jihar Legas

Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya sanar da sassauta dokar hana fita da ya saka a jihar sakamakon rikicin da ya barke a zanga-zangar #EndSARS.

Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne a yayin da yake wa jama’ar jihar bayani a yammacin ranar Juma’a.

“Jihar nan jiha ce da ake gudanar da abubuwa tsawon sa’o’i 24, dan haka muna fatan komai zai koma yadda yake a baya”, Inji Sanwo-Olu.

Ya ce mutanen jihar suna da damar yin al’amuransu daga karfe 8 na safe zuwa karfe 6 na yamma a kullum.

Gwamnan ya kara da cewa zasu ci gaba da bibiyar yadda al’mura suke tafiya, domin tabbatar da doka a jihar.