Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya sanar da sassauta dokar hana fita da ya saka a jihar sakamakon rikicin da ya barke a zanga-zangar #EndSARS.
Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne a yayin da yake wa jama’ar jihar bayani a yammacin ranar Juma’a.
- Zanga-zangar EndSARS ta jawo asarar biliyan N400 a Legas
- Zalunci: An fitar da sunayen ’yan sandan da za a hukunta
- ‘Labarun karya ne suka haifar da rikici a Legas’
“Jihar nan jiha ce da ake gudanar da abubuwa tsawon sa’o’i 24, dan haka muna fatan komai zai koma yadda yake a baya”, Inji Sanwo-Olu.
Ya ce mutanen jihar suna da damar yin al’amuransu daga karfe 8 na safe zuwa karfe 6 na yamma a kullum.
Gwamnan ya kara da cewa zasu ci gaba da bibiyar yadda al’mura suke tafiya, domin tabbatar da doka a jihar.