Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Radda ya bai wa Hukumar ƙididdiga ta jihar damar gudanar da ƙidayar almajirai da makarantun Islamiyya a jihar.
Babban jami’in ƙididdiga na jihar, Farfesa Saifullahi Sani wanda ya bayyana hakan a Katsina ranar Alhamis, ya ce maƙasudin gudanar da ƙidayar shi ne tsara dabarun inganta tsarin.
- ’Yan sanda sun kashe ’yan fashi da ƙwato makamai a Kaduna
- An tallafawa iyalan ’yan sanda da Naira miliyan N13.4m a Borno
Babban jami’in ƙididdigar ya bayyana hakan ne yayin wani muhimmin taro na yini ɗaya da masu ruwa da tsaki a jihar.
Sani ya ce, “Manufofin ƙidayar sun haɗa da samar da cikakkun bayanai na dukkan Makarantun Alkur’ani da kuma samar da cikakken tsarin yaran da ba su zuwa makaranta a jihar.
“Manufofin hakan su ne, a tabbatar da halin da ɗaliban suke ciki, don sanin halin da suke ciki, da samun cikakkun bayanai na malaman makarantun.
“Haƙiƙa wannan an yi shi ne don samun cikakkun bayanai na ɗalibai a fannin.
“Haka kuma don tabbatar da adadin ɗaliban da suka tsunduma cikin harkar bara a jihar da kuma taimakawa wajen fahimtar hanyoyin aiwatarwa a halin yanzu, gano giɓi da jagoranci wajen samar da matakan da suka dace.”
Ya bayyana cewa, sakamakon ƙidayar zai sanar da shiga tsakani da kuma fara ƙoƙarin da suka dace na sauya tsarin karatun Alkur’ani a halin yanzu.