Gwamnatin Kano ta tsawaita hutun da ta bayar na Karamar Sallah domin ba wa al’ummar Musulmi damar ci gaba da shagulgulan sallar a Jihar.
Da farko an ware ranakun Laraba da Alhamis a matsayin hutu amma aka tsawaita zuwa Juma’a bayan an yi Sallah a ranar Alhamis.
- An kara kona ofishin ’yan sanda a Abiya
- Janar Dogonyaro: Buhari na alhinin mutuwar sojan da ya yi jawabin yi masa juyin mulki
Kwamishinan Yada Labaran Jihar Kano, Muhamamd Garba ya sanar a ranar Alhamis cewa yin hakan ya zama dole saboda ranar Laraba da tun farko aka bayar hutu ta zama ranar 30 na watan Ramadan.
Sanarwar ta mika sakon Gwamna Abdullahin Ganduje na fatan alheri ga al’ummar Jihar a yayin da suke ci ga da shagulgulan sallah, wanda ya bukace su da su yi amfani da bikin sallar wajen neman kusanci da Allah.
Ganduje ya kuma roki Kanawa da su yi amfani da musamman lokacin Sallar Juma’a wajen neman yin addu’o’in neman zaman lafiya da aminci a fadin Najeriya.