✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Kano ta rufe masallacin Sheikh Abduljabbar kan ‘batanci ga Sahabbai’

Ta hana malamin yin wa'azi ko lakca tare da dakatar da sanya karatunsa a kafafen yada labarai.

Gwamnatin Kano ta rufe masallacin fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, bisa zargin malamin da yin izgili ga Sahabban Manzon Allah (SAW).

Gwamnatin Jihar ta rufe daukacin cibiyoyin karatu da majalisin Sheikh Abduljabbar, ta hana shi gabatar da wa’azi ko lakca; sannan ta dakatar da kafafen yada labarai daga sanya karatuttukansa ko hudubobi ko da’awa.

Sanarwar da Kwamishinan Yada Labaran Jihar Kano, Muhammad Garba ya fitar da sanyin safiyar Alhamis ta ce, “An samu rahoton kalamai na rashin kan gado da tunzura jama’a da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ke yi.

“An ba da umarnin gaggauta rufe masallaci da cibiyar da Abduljabbar yake gudanar da harkokinsa da ke filin Mushe da kuma fadin jihar nan.

“Majalisar Zartarwar Jihar Kano ta umarci Abduljabbar da ya daina wannan kalamai na rashin kan gado.

“Majalisa ta sake umartar kafafen yada labarai da na zumunta da su dakata da saka karatun Abduljabbar har tsawon lokacin da za a gama bincike, don samar da zaman lafiya a Jihar Kano,” inji sanarwar wadda ta ce an dauki matakin ne a taron Majalisar Zartar Jihar.

Kazalika Gwamnatin Kano ta umarci jami’an tsaro su gunadar da cikakken bincike don hukunta duk wani da aka samu da aikata kalamai irin na Abduljabbar.

Gwamnatin ta ba da umarnin rufe masallacin malamin da ke Karamar Hukumar Gwale a Jihar, tare da hana malamin yin duk wani wa’azi ko lakca.

Gwamnatin ta ba wa Kwamishinan ’yan sandan jihar, umarnin yin bincike tare da tabbatar da kowane cikakken bin dokar gwamnatin jihar.

Zuwa yanzu dai ba mu samu jin ta bakin malamin ko mabiyansa ba.

Sabanin Sheikh Adbuljabbar

Malamai na ganin akidar Sheikh Abduljabbar ta saba wa ‘Jamhur’, ta yadda suke bayyana wasu karatuttukansa a matsayin batanci ga Sahabban Manzon Allah (SAW) da sauran manyan magabata na kwarai.

Sahabbai da Tabi’ai da mabiya bayansu, musamman malaman da aka assasa mazhabobin Fikihu su ne manyan ababen koyi ga Musulmai bayan Alkur’ani da Sunnar Manzon Allah (SAW).

Sheikh Abduljabbar, wanda mabiyin darikar Kadiriyya ne na kuma sukar Sahabbai da zargin su da kirkirar Hadisai suna dangantawa da Manzon Allah (SAW); yana kirar mabiyansa da su yi watsi da Hadisan.

Malaman Kano sun yi kashedi

A baya-bayan nan malamai mabiya wasu dariku a Kano sun yi ta la’antar karantarwar ta Abduljabbar, inda suka kamanta akidarsa da ta Shi’a tare da kiran Gwamnatin Jihar Kano ta taka masa burki.