Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya kara ranar Litinin cikin jerin ranakun da za a iya fita domin gudanar da harkoki a jihar.
Babban Mai Taimaka wa Gwamnan a bangaren hulda da ‘yan jaridu, Abba Anwar shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai da yammacin Lahadi.
Da wannan karin yanzu mutanen Kano za su rika fita ke nan a ranaku hudu a mako —kari a kan ranakun Laraba, Juma’a da kuma Lahadin da aka fara sassautawa.
Sanarwar ta ce Gwamna Ganduje ya amince mutane su rika fita daga 6.00 na safe zuwa 6.00 na yamma don yin hada-hada a ranakun hudu, har zuwa sadda za a janye dokar kulle a jihar.
Gwamnatin Jihar ta kuma ja hankalin al’umma da su ci gaba da kiyaye dokokin da masana kiwon lafiya su ka ba da shawara.
“Dole mutane su ci gaba da amfani da kyallen rufe fuska, bayar da tazara, amfani da sinadarin tsaftace hannu tare da wanke hannuwa a ruwa mai gudana”, inji sanarwar.
Gwamnatin ta cikin sanarwar ta kuma ce, “Mun umarci dukkan kasuwanni da sauran wuraren taruwar jama’a da su tabbatar ana kiyaye wadannan dokokin har zuwa lokacin da za mu kai ga fatattakar cutar [coronavirus] daga jiharmu”.
A ‘yan kwanakin nan dai a jihar ta Kano an sami ragi matuka a yawan sabbin mutanen da ke kamuwa da cutar coronavirus duba da alkaluman da aka rika samu ‘yan makonnin da su ka gabata.