Gwamnatin Jihar Kano, ta janye dokar hana fita da ta sanya, biyo bayan zanga-zangar matsin rayuwa da ta rikiɗe zuwa tarzoma a jihar.
Wannan na cikin wata sanarwa da Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Baba Halilu Ɗantiye, ya fitar da yammacin ranar Litinin.
- Ambaliyar ruwa ta shafe hanyar Jigawa zuwa Bauchi da Gombe
- Zanga-zanga: ’Yan Sanda sun cafke mutum 873 a Kano
Idan ba a manta ba, Aminiya ta ruwaito yadda gwamnatin jihar, ta sanya dokar hana fita a jihar bayan da zanga-zangar da aka fara a ranar 1 ga watan Agusta, a faɗin ƙasar kan tsadar rayuwa ta koma tarzoma.
Daga baya Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf, ya sassauta dokar daga ƙarfe 8 na safe zuwa ƙarfe 2 na rana.
Har wa yau, gwamnatin ta sake sassauta dokar daga ƙarfe 6 na safe zuwa 6 na yamma.
Ɗantiye, ya ce gwamnatin ta janye dokar ne gaba ɗaya, duba da yadda al’amura suka daidaita a jihar.
Kazalika, Kwamishinan ya buƙaci al’ummar jihar da su ci gaba da kasancewa masu bin doka da oda.
Sannan ya roƙi su yi Kano addu’a domin samun dawamammen zaman lafiya da kuma ƙasa baki ɗaya.
Idan ba a manta ba, zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa ta fara ne a ranar 1 ga watan Agusta a faɗin Najeriya.
Sai dai zanga-zangar a jihohin Kano, Katsina, Kaduna, Jigawa, da wasu sassan Najeriya sun rikiɗe zuwa tarzoma.
Lamarin ya janyo asarar rayuka da dukiya mai tarin yawa.
Daga bisani Shugaba Tinubu ya yi wa ‘yan Najeriya jawabi game da halin da suke ciki, amma jawabin bai gamsar da masu zanga-zangar ba.
Lamarin da ya ƙara rura wutar zanga-zangar a wasu yankuna, sai dai jami’an tsaro sun kame da dama da suka fake da zanga-zangar wajen tada fitina.