Gwamnatin jihar Kaduna ta rusa ginin otal din da aka zaba domin gudanar da wani taron badala da wasu matasa suka shirya yi a jihar.
A cikin makon nan ne wata fasta ta karade kafafen sada zumunta na zamani dauke da tallan taron wanda aka tsara zai gudana ranar 27 ga watan Disambar 2020, inda ake sa ran gudanar da shi tsirara, yayin da mahalartansa kuma za su yi jima’i da juna.
- An cafke wadanda suka shirya casun jima’i a Kaduna
- Buhari zai yi wa ’yan Najeriya jawabi ranar Juma’a
Sai dai daya daga cikin na gaba-gaba a wadanda suka kirkiri taron ya ce sun shirya shi ne a matsayin raha tsakaninsa da abokansa.
Kakakin Hukumar Tsara Birane ta Jihar Kaduna (KASUPDA) Nuhu Garba shine ya tabbatar wa da Aminiya rushe ginin otal dake unguwar Sabon Tasha a Kaduna.
Ya ce an rusa shi ne la’akari da dokokin da suka kafa hukumar.
“Doka ta ba KASUPDA damar rusa kowanne gini da ya saba tanadin yin sa. Idan alal misali aka mayar da gidan kwana wani abin na daban, muna da ikon rusa shi, musamman in abinda ake yi ya saba da bukatun jama’a.
“Yanzu haka kuma muna unguwar Narayi domin aiwatar da makamancin wannan aikin. Yanzu haka muna rushe wani gidan da yake yada ayyukan badala,” inji kakakin KASUPDA.
A wani labarin kuma, daya daga cikin wadanda Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta yi bajekolinsu a cikin masu shirya taron ranar Alhamis ya ce ba su shirya taron ba ne da nufin zubar da mutuncin jihar, hasali ma iya abokansu suka shirya kuma bai kamata abin ya shiga duniya ba.
A cewar wanda ake zargin, “Mun fara shirya shi ne a tsakanin abokan mu. Kawai wata a cikinmu ta dauki fastar sa ta wallafa a shafin Twitter.
“Ba mu taba wallafa su a Twitter ba. Hakika ni ne na kirkiri taron, amma ba don na muzgunawa kowa a Kaduna na yi hakan ba.
“Gaba daya abin fa wasa ne, kawai wani abokinmu ne yaje ya yi fasta sai ya tura wani, shi ma ya kara turawa wani, ta haka abin ya yadu har ya je Twitter,” inji shi.
Sai dai da aka tambayi wanda ake zargin sunansa ya ki amincewa ya fada.